fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Matsin tattalin arziki

Da yawan mutane basu san me ake nufi da shiga ko fita daga matsin tattalin arziki ba saboda kullun a cikinsa suke>>Sanata Shehu Sani

Da yawan mutane basu san me ake nufi da shiga ko fita daga matsin tattalin arziki ba saboda kullun a cikinsa suke>>Sanata Shehu Sani

Uncategorized
A yayin da Najeriya ta tsunduma cikin matsin tattalin arzikin da ba'a taba ganin irinsa ba, shekaru 33 da suka gabata, 'yan Najeriya na ta martani akan lamarin.   Sanata Shehu Sani na daga cikin wanda suka bayyana ra'ayinsu kan wannan abu.   Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, da yawan mutane basu san yanda ake shiga ko fita daga matsin tattalin arziki ba saboda kullun su a cikinsa suke dindindin. Actually,many people don’t know what is to be in or out of recession because they permanently reside in it.
Akwai yiyuwar Najeriya ta fada matsin tattalin arziki da sakamako mummuna>>Shugaba Buhari

Akwai yiyuwar Najeriya ta fada matsin tattalin arziki da sakamako mummuna>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai yiyuwar Najeriya ta fada matsin tattalin arziki wanda rabon a ga irinsa tun shekaru 4 da suka gabata.   Shugaban ya bayyana hakane a yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2021 ga majalisar tarayya a yau, Alhamis inda ya gabatar da kasafin kudin na Tiriliyan 13.1. Ya bayyana cewa akwai kuma gibin tiriliyan 4.8 a kasafin kudin Wanda da bashine za'a cikeshi.   Yace Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 tawa tattalin arzikin Najeriya illa sosai amma duk da haka kokarin gwamnati yasa munin matsin tattalin arzikin bai kai na sauran kasashe masu tasowa ba.   Yace Najeriyar ka iya fadawa matsin tattalin arziki saboda darajar kayan da take fitarwa sun yi kasa saidai yace gwamnati na iya bakin kokarinta dan ...
Najeriya zata tsunduma matsin tattalin arziki amma ba zata dade ba zata fito>>Ministar Kudi

Najeriya zata tsunduma matsin tattalin arziki amma ba zata dade ba zata fito>>Ministar Kudi

Siyasa
Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa Najeriya zata tsunduma matsin tattalin arziki amma ba zata dade ba zata fito.   Ta bayyana hakane bayan taron iyayen kasa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya wanda tsaffin shuwagabannin Najeriya in banda Olusegun Obasanjo suka halarta a fadarshi a Abuja. Tace duk da gwamnati ta zuba triliyan 2.3 dan farfado da tattalin arzikin amma cikin watanni 3 masu zuwa za'a tsunduma matsin tatgalin arziki, saidai tace kokarin da suke ba zai bari a dade cikin matsin tattalin arzkin ba. Hutudole ya kuma fahimci babban bankin Najeriya CBN zai fara sayar da dalar Amurka ga 'yan Canji masu lasisi.   Sannan ya bada umarnin su rika sayar da dalar akan Naira 386.
Da wuya gwamnati ta iya biyan bashin data ciwo saboda karayar tattalin Arziki>>Masana

Da wuya gwamnati ta iya biyan bashin data ciwo saboda karayar tattalin Arziki>>Masana

Siyasa
A jiyane muka ji yanda tattalin arzikin Najeriya ya samu tawaya kamar yanda NBS ta bayyana. Rahoton nata yace tattalin arzikin ya samu tawaya da kaso 6.1 cikin 100 a watanni 3 da suka gabata.   Saidai masana sun bayyana abinda hakan ke nufi. Shugaban kungiyar masu masana'antu ta Najeriya, MAN, Ambrose Oruche ya bayyana cewa hakan na nufin da wuya gwamnati ta iya samun kudin shigar da zata biya bashin data ciwo wanda zai kuma bata dama har ta ci gana da ayyukan dake gabanta.   Yace dorawa mutane karin haraji ba shine mafita ba ya kamata ace an samo wata hanya ta karin samun kudin ahigar gwamnati musamman yanzu da take son kara ciwo wasu basukan.   Shima dai shugaban hukumar kasuwanci ta jihar Legas, Muda Yusuf yace ya kamata gwamnati ta yi wani abu akan hauh...
Najeriya ka iya sake fadawa cikin wani sabon matsin tattalin arziki>>Gwamnatin tarayya

Najeriya ka iya sake fadawa cikin wani sabon matsin tattalin arziki>>Gwamnatin tarayya

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa Najeeiya ka iya sake fadawa cikin wani sabon matsin tattalin arziki.   Hakan ya fito ne daga bakin Ministar kudi, Zaiban Shamsuna Ahmad yayin wani taro kan bayanin tattalin arziki da tsare-tsaren gwamnatin. Hutudole ya ruwaito,Ministar da karamin Ministan kudi, Clement Agba ya wakilta tace Rahoton watanni 3 na 2 na wannan shekarar bai zoma Najeriya da dadi ba dan hakane take fatan Rahoton watanni 3 na 3 yazo da kyau. Tace idan wannan Rahoto bai zo da kyau ba to kasar zata fada matsin tattalin arziki irin na shekaru 4 da suka gabata.
Najeriya zata sake dulmuya cikin wani matsin tattalin arziki>>Gwamnatin tarayya

Najeriya zata sake dulmuya cikin wani matsin tattalin arziki>>Gwamnatin tarayya

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa nan da watanni 3 na karshen shekararnan kasar zata sake dulmiya cikin wani matsin tattalin arziki.   Gwamnati ta danganta rashin samun gabakar kayan da kasar ke fitarwa da kuma karancin kudin shiga akan wannan matsin tattalin arziki da za'a shiga. Tace lamarin ma ya zarce yanda ta yi hasashe. Ministar kudi da tsara kasafin kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka inda tace ko za'a sake shiga wani matsin tattalin arzikin bayan shekaru 4.   Tace wannan karin akwai mummunan sakamako da matsin tattalin arziki zai jawowa Najeriya.
Dalilin da yasa ba zamu taba iya daina ciwo Bashi ba>>Ministar Kudi

Dalilin da yasa ba zamu taba iya daina ciwo Bashi ba>>Ministar Kudi

Siyasa
Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa matsalolin zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 da ya jefa 'yan Najeriya da tattalin arziki cikin halin kaka nikayi da kuma faduwar darajar Man Fetur wanda daga shine Najeriya ke samun kudin shiga yasa dole gwamnati ta ci gaba da ciwo bashi ido rufe.   Tace akwai tsare-tsare da ta fito dashi dan samawa gwamnati kudin shiga wanda ba ta hanyar Mai ba. Me baiwa shugaban kasa,Muhammadu Buhari shawara ta fannin Tattalun arziki da kudi, Mrs.Sarah Alade ce ta wakilci Zainab Ahmad a wani taro da aka yi na tattalin arziki ta kafar sadarwar Zamani.   Tace akwai tsare-tsare da gwamnati ta yi na farfado da tattalin arziki wanda idan ba ta ciwo bashi ba ba zasu yiyu ba. Tace amma idan 'yan Najeriya zasu bada hadin kai wajan b...
Yawan talakawa fitik zasu karu a Najeriya zuwa Miliyan 95.7 nan da shekarar 2022>>Bankin Duniya

Yawan talakawa fitik zasu karu a Najeriya zuwa Miliyan 95.7 nan da shekarar 2022>>Bankin Duniya

Uncategorized
Rahotanni daga bankin Duniya na cewa mutane Miliyan 95.7 ne zasu afKa cikin matsanancin Galauci a Najeriya nan da shekarar 2022.   Rahoton yace bullar cutar Coronavirus/COVID-19 ya taimakawa karin talakawan na Najeriya wanda kamin zuwan cutar an yi kiyasin cewa mutane Miliyan 90 ne zasu shiga talaucin amma a yanzu bayan zuwan cutar, sun karu da mutane miliyan 6. Rahoton yace mutanen da a yanzu suke bakin gabar fadawa matsanancin talauci dake rayuwa sama da dalar Amurka 1 a Ranar zasu fada talaucin nan bada dadewa ba.   Rahoton yace mutane Miliyan 90.2 ne zasu fada talaucin a wannan shekarar ta 2020 yayinda zasu karu zuwa miliyan 95.7 a shekarar 2022.
Za’a samu Matsin tattalin arziki a Najeriya da aka shekara 40 ba a ga irinshi ba>>Bankin Duniya

Za’a samu Matsin tattalin arziki a Najeriya da aka shekara 40 ba a ga irinshi ba>>Bankin Duniya

Siyasa
Bankin Duniya yayi gargadin cewa Najeriya zata ga matsin tattalin Arziki da aka shekara 40 ba a ga irinshi ba dalilin cutar Coronavirus/COVID-19 da kuma faduwar farasin mai a kasuwannin Duniya.   Rahoton da ya fita a yau, ya bayyana cewa Najeriya zata ga faduwar da kaso 3.2 kuma idan ba ta yi wani abu ba kan dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 to munin matsin tattalin arzikin zai karu. Kamin a shiga Annobar cutar Coronavirus/COVID-19,  Najeriya an mata hasashen zata samun tagomashin tattalin arziki da kaso 2.1.   Wakilin bankin Duniya a Najeriya,  Shubham Chaudhuri ya bayyana cewa, ya bayyana cewa ba'a san iya tsawon lokacin da illar da Coronavirus/COVID-19 tawa tattalin arzikin Duniya zai kwaranye ba amma akwai bukatar Najeriya ta tashi tsaye wajan farfa...
Matsin tattalin Arziki:Buhari ya dakatar da ma’aikatun gwamnati daga siyo sabbin Motoci

Matsin tattalin Arziki:Buhari ya dakatar da ma’aikatun gwamnati daga siyo sabbin Motoci

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta dakatar da siyo sabbin motoci dan tabbatar da ganin an farfado da tattalin arzikin Najeriya.   Wannan na daya daga cikin tsare-tsaren tada komadar tattalin arziki da kwamitin tattalin arziki karkashin mataimakin shugaban kasa,Farfesa Yemi Osinbajo suka bada shawarar aiwatarwa. Me magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesinane ya bayyana haka inda yace shugaba Buhari ya amince da wannan shawara inda motocin kwana-kwana dana daukar marasa lafiya da sauran masu muhimmanci ne kawai za'a ci gaba da siyowa.   Ya kuma kara da cewa akwai tsarin fadada tallafin da ake baiwa mutane, da tallafi ga kananan 'yan kasuwa da fadada harkar Noma da sauransu.