fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Mikel Arteta

Antonio Conte ya amince ya mayewa Arsenal gurbin kocinta Mikel Arteta

Antonio Conte ya amince ya mayewa Arsenal gurbin kocinta Mikel Arteta

Wasanni
Arsenal ta kammala yarjejeniya da Antonio Conte, yayin da kocinta Mike Arteta ke cigaba da shan gwagwarmaya a wannan kakar. Arsenal ta kasance a kasan teburin gasar Firimiya bayan ta fadi gabadaya wasanni uku data fara bugawa a wannan kakar ba tare da cin ko kwallo guda ba. Inda darektan kungiyar Edu da sauran shuwagabanninta suke cigaba da baiwa Arteta dama, amma fa da alamu yanzu ya kaisu makura. Inda Arsenal ta fara shirin maye gurbinshi, kuma idan har ta soke mai kwantiraki a makonni masu zuwa to Conte ne zai cigaba da horas da ita, inda shi ya kasance bashi da aiki tun bayan daya bar Inter Milan. Conte agrees on terms with Arsenal to replace Arteta Arsenal have agreed terms in principle with Antonio Conte, as Mikel Arteta continues to struggle this season, according to ...
Arsenal tana bukatar kara siyan wasu yan wasa kafin ta fara takarar lashe kofin Premier league>>Arteta

Arsenal tana bukatar kara siyan wasu yan wasa kafin ta fara takarar lashe kofin Premier league>>Arteta

Wasanni
Kocin Arsenal, Mikel Arteta wanda ya maye gurbin Unai Emery a shekara ta 2019 har yayi nasarar lashe kofuna biyu a kungiyar wanda suka hada da FA Cup da kuma Community Shield a shekara ta farko daya a kungiyar. Amma sai dai Arsenal bata lashe babban kofin kasar Ingila ba har na tsawon shekaru 14 tun lokacin da Arsene Wegner ya ci masu kofin shekara ta 2004. Kuma duk da cewa Arteta ya siyo Partey a da kuma Gabriel, har yanzu baya jin cewa kungiyar Arsena zata iya lashe kofin Premier league. Yayin daya bayyana cewa "Arsenal tana bukatar kara siyan wasu yan wasa kafin ta fara takarar lashe kofin Premier league, saboda akwai wasu kungiyoyi na gasar wanda sai ka dauki lokaci kafin ka kai matakin su".
Mikel Arteta yace ilimintar da yan wasan premier lig gami da cutar Covid-19 na da matukar muhimmanci

Mikel Arteta yace ilimintar da yan wasan premier lig gami da cutar Covid-19 na da matukar muhimmanci

Wasanni
An dakatar da wasannin kwallon kafa a kasar ingila saboda rikicin cutar coronavirus, amma an samu labari ranar talata cewa ministoci suna iya bakin kokarin su domin suga cewa an cigaba da buga wasannin yayin da gwamnatin kasar ke shirin sassauta dokar zaman gida. Shugaba Arsenal Arteta wanda bai dade da warkewa daga cutar ba yace babbar matsalar da premier lig zasu fuskanta wajen dawowa shine ilimintar da yan wasan su da kuma sauran ma'aikatan su gami sababbin sharuddan cutar Covid-19. Daya daga cikin dokokin da premier lig tasawa yan wasan ta shine zasu rufe fuskokinsu idan aka cigaba da yin atisayi, yayin da suma kungiyoyin nasu zasu siyo abun rufe fuskan dayawa su ajiye saboda tsaro.
Mikel Arteta zai siyar da wasu yan wasan shi 2 dan yiwa Aubameyang sabuwar kwangila

Mikel Arteta zai siyar da wasu yan wasan shi 2 dan yiwa Aubameyang sabuwar kwangila

Wasanni
Manajan Arsenal Mikel Arteta ya san cewa in har suka ce zasu yiwa Aubameyang sabuwar kwangila to zata yi tsada saboda haka ne suka yanke shawarar siyar da yan wasan su har guda biyar domin su cigaba da wasa tare da tauraron nasu. Kwangilar Aubameyang zata kare ne nan da shekara daya kuma Arsenal suna tattaunawa gami da sabuwar kwangilar da zasu yi mai no kuma su siyar da shi a wannan kakar wasan inba haka ba zai bar kungiyar a kyauta da zarar kwangilar shi ta kare. Arsenal zasu iya karama tauraron nasu kwangilar shi in har suka siyar da Shkodran Mustafi da Henrikh mkhitariyan a wannan kakar wasan a cewar tsohon dan wasan su da kuma dan wasan Scotland da mai yin sharhin wasanni kwallon kafa Charlie Nicholas. Arsebal sun siyo Aubameyang ne daga Borussia Dortmund a shekara ta 2...
Mikel Arteta ya warke daga coronavirus

Mikel Arteta ya warke daga coronavirus

Kiwon Lafiya
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce ya warke sarai daga coronavirus da ya kamu da ita.     Dan kasar Spaniya, mai shekara 37, ya zama kocin Premier na farko da ya kamu da coronavirus ranar 12 ga watan Maris.     Kocin ya sanar da baya jin dadin jikinsa, bayan da aka tabbatar ya yi cudanya da mai Olympiokos, Evangelos Marinakis wanda ya kamu da cutar ranar 10 ga watan Maris, inda Arsenal ta buga Europa League da kungiyar ta Girka.     Arteta ya ce ''Sai da na yi kwana uku zuwa hutu ina jinya sannan na fara jin karfin jikina, daga nan alamun cutar ya bace''     Ranar Talata ya kamata 'yan wasan Arsenmal su koma atisaye, bayan da aka killacesu mako biyu, saboda samun Arteta da coronavirus, an kuma dage ranar da za su koma...