
Hotuna:Sarkin Kano ya kaiwa Tsaffin shuwagabannin kasa, Janar IBB da Abdulsalam ziyara
Me martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya kaiwa tsaffin shuwagabannin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da janar Abdulsalam Abubakar ziyara a gidajensu dake Minna.
Sarkin ya kai ziyarar ne bisa jagorancin me martaba sarkin Minna, Dr. Umar Farouk Bahago.