
Mohamed Salah na shan suka daga wajan Musulmai bayan da yayi Murnar Kirsimeti
Tauraron dan kwallon kasar Egypt me bugawa kungiyar Liverpool wasa, Mohamed Salah ya taya Kiristoci Murnar ranar Kirsimeti.
Salah tare da iyalansa sun saka kayan bikin Kirsimeti inda ya saka a shafinsa na sada zumunta. Saidai wasu daga cikin Musulmai basu ji dadin hakan ba inda suka rika cewa bai kamata ba.
Wani da ya bayyana ra'ayinsa akan hoton na Salah, ya saka Bidiyon wani mutum da yayi kokarin shiga wat kofa ta ki budewa, inda ya ce Salah ne yayin da yake kokarin shiga kofar Aljannah.
https://twitter.com/Hanaddo1/status/1342229705982959618?s=19
Wani kuwa me sunan Smiley ya bayyana cewa shiyasa yake son dan damben nan, Khabib Nurmagomedov a duk cikin shahararren mutane Musulmai, saboda ba zai taba yin wasa da addininsa ba dan farantawa wani, ya...