
Motsa Jiki dake karawa mata ni’ima da karfin Jima’i ga maza
Akwai nau'ukan motsa jiki da dama, amma akwai na musamman da suka shafi ƙarin lafiya ga rayuwar jima'i ga ɗan Adam.
Motsa jiki wani ɓangare ne na musamman na kiwon lafiya wanda yin sa ke tasiri ga ƙara ƙoshin lafiya, rashinsa kuma ke zama illa ga lafiyar.
Motsa jiki kan kasance maganin cututtuka da dama, waɗanda likitoci ke bai wa mutane shawara su dinga motsa jikinsu saboda muhimmancinsa ga lafiya.
Ƙwararren likitan motsa jiki (Physiotherapist) Dakta Abubakar Ahmad Tsafe na babban asibitin Farida da ke Gusau a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, ya yi bayani kan wani nau'in motsa jiki da ya shafi lafiyar jima'i da inganta al'aurar maza da mata.
Likitan ya ce irin motsa jikin zai taimaka wa maza magance matsalar saurin inzali...