
Bidiyon yanda Dembele ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da Atisaye
Tauraron dan kwallon Atletico Madrid, Moussa Dembele ya yanke jiki ya fadi kasa yayin da suke Atisaye shi da abokan aikinsa.
Dembele na Aro ne daga Lyon wanda kuma zuwa yanzu wasanni 4 ya bugawa Atletico Madrid. Wannan yasa wasu ke ganin cewa bai taka rawar gani ba. Atletico Madrid na da damar sayensa idan suna so.
Lamarin ya farune ranar Talata da yamma sanda suke Atisaye.
Daga baya dai likitoci sun dubashi kuma ya dawo hayyacinsa wanda ma da kanshi ya tuka motarsa zuwa gida.
https://www.youtube.com/watch?v=EOQ5IaepIB0