
Hotuna: Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yaje gaisuwar Sarkin Zazzau
Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya je Kaduna dan zuwa Zaria gaisuwar Marigayi tsohon Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.
Sarki Sanusi ya taso daga Legas ne zuwa Kaduna. Hakanan ana tsammanin a yau dinne, a matsayinsa na mataimakin hukumar kula da zuba jari ta jihar Kaduna, zai gabatar da jawabi a wajan taron tattalin arziki da kula da zuba jari na jihar.