fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Muhammad Buhari

“Kunada saurin mantuwa ne amma munyi iya bakin kokarinmu kan matsalar tsaro>>Shugaban Buhari ya fadawa ‘yan Najeriya masu yin korafi akan kashe-kashe

“Kunada saurin mantuwa ne amma munyi iya bakin kokarinmu kan matsalar tsaro>>Shugaban Buhari ya fadawa ‘yan Najeriya masu yin korafi akan kashe-kashe

Siyasa, Tsaro, Uncategorized
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yan Najeriya nada sauran mantuwa, bayan da suke tayin korafe korafe akan matsalar tsaro domin sun mance matsalar tsaron da kasar ke fama da shi kafin ya karbi mulki. Inda yace gwamnatin shi tayi iya bakin kokarinta akan matsalar tsaro. Buhari ya bayyana hakan ne a taron daya halatta na majalisar zartaswa. Muhammadu Buhari ya zamo shugaban kasar Najeriya ne a shekarar 2015 karkashin tutar APC kuma yayiwa kasar alkaura wanda suka hada da magance maysalar tsaro. Amma yanzu kasar na cigaba da fama da matsar tsaro yayin da garkuwa da mutane ya zamo ruwan dare a fadin kasar bakidaya.  
Shugaban kasa Buhari ya aike da sakon ta’aziyya Bisa rasuwar Shehun Malami Skeik Lemu

Shugaban kasa Buhari ya aike da sakon ta’aziyya Bisa rasuwar Shehun Malami Skeik Lemu

Uncategorized
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa game da rasuwar wani malamin addinin Islama, Sheikh Ahmed Lemu. Shugaba Buhari ya bayyana Sheik Ahmed Lemu a matsayin "fitaccen malami, masanin shari'a, kuma marubuci wanda al'umma ta amfana da Dumbin iliminsa.   Hakan na kunshene ta cikin sanarwar da babban mataimaki na musamman ga Shugaban kasa Malam Garba shehu ya fitar a ranar Al'hamis. Inda ya bayyana mutuwar malamin a matsayin wani babban rashi da a kai wa kasa dama Afirka baki daya.     A cewar Shugaba Buhari Gudunmwar da Margayin ya bayar abar a yaba ne inda ya bayyana cewa tabbas ba za'a taba mantawa da irin gudunmawar da shehun malamin ya  bayar ba ta fuskar addini da zaman lafiya.
Hotuna:Gwamna Matawalle ya gabatarwa da shugaba Buhari Gwal din da aka hako a Zamfara

Hotuna:Gwamna Matawalle ya gabatarwa da shugaba Buhari Gwal din da aka hako a Zamfara

Siyasa
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa dake Abuja a daren jiya.   Gwamnan ya gabatarwa da shugaban kasar gwala-gwalan da aka hako a Zamfara da sauran wasu ma'adanai. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1298159981783547904?s=19 Hadimin shugaban masar, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka ta shafinsa na Twitter. https://twitter.com/Bellomatawalle1/status/1298129365985906693?s=19 Shima Gwamna Matawalle ya bayyana hakan.  
Shugaban kasa Buhari yayi sabon nadi

Shugaban kasa Buhari yayi sabon nadi

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Adesoji Adesugba, a matsayin sabon Manajan Daraktan cibiyar kasuwanci ta Najeriya (NEPZA). NEPZA cibiya ce da ke karakashin ma'aikatar kasuwanci da zuba hannun jari. An tabbatar da nadin Adesugba a wata wasika da shugaban ma’aikatan Buhari, farfesa Ibrahim Gambari ya sanya wa hannu, ya kamu aikewa ministan ma'aikatar. Sanarwa daga maimagana da yawun ministan kasuwanci da saka hannun jari Otunba Richard Adeniyi Adebayo, ya yaba wa Buhari kan nadin Adesugba. Haka zalika ministan ya yaba tare da nuna jin dadinsa bisa zabin Adesuga a matsayin Daraktan cibiyar, inda ya tabbatar da cewa tabbas ya cancanta duba da irin kwarewarsa. Farfesa Adesugba ya fara aiki a hukumar kwastam da mukamin sufeto II a shekarar 1982 kafin daga...
Shugaba Buhari ya maye sunan mataccen daya baiwa Mukami da wani me rai

Shugaba Buhari ya maye sunan mataccen daya baiwa Mukami da wani me rai

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye sunan mataccen da a baya ya baiwa mukami a hukumar raba daidan mukaman gwamnati ta FCC da wani me rai.   A baya dai munji cewa shugaba Buhari ya baiwa Tobias Chukwuemeka mukami amma daga baya aka gano cewa ya mutu tun a watan Fabrairu da shekaru 59. Tobias tsohon dan majalisar wakilai ne.   A wasu sunaye 4 da shugaba Buhari ya aikewa majalisar dattijai dan maye gurbinsu a cikin kwamitin hadda sunan Tobias a cikin wanda za'a maye din.   Kakakin majalisar dattijai,Ahmad Lawal ne ya bayyana sunayen mutanen 4 da shugaba Buhari ya aike musu a zaman na majalisar na jiya, Talata, 12 ga watan Mayu wanda suka hada da Moses A. (Delta), Afamefuna Osi (Ebonyi), Wasiu Kayode (Lagos), Alakayi Mamman (Nasarawa).
Rashin iya aikin Buhari da saka ido akan abubuwa ne yasa Cutar Coronavirus/COVID-19 ta yi tsanani sannan kuma ma’aikatanshi ke ta sace kayan tallafin da za’a ba talakawa ba tare da ya sani ba>>PDP

Rashin iya aikin Buhari da saka ido akan abubuwa ne yasa Cutar Coronavirus/COVID-19 ta yi tsanani sannan kuma ma’aikatanshi ke ta sace kayan tallafin da za’a ba talakawa ba tare da ya sani ba>>PDP

Siyasa
Jam'iyyar PDP ta caccaki ssalon shugaban kasa,Muhammadu Buhari na yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 inda tace salon mulkinsa na zama a can fadarshi ba tare da ya san anahin abinda ke faruwa da cikin kasar ba ke sa ake samun matsala wajan yaki da cutar.   PDP ta bakin sakataren watsa labaranta, Kola Ologbondiyan ta bayyana cewa cutar Coronavirus/COVID-19 ta kara munana a Najeriya ne saboda rashin iya mulki na shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  tace da ace an samu shugaba wanda yake da jajircewa da abubuwa basu tabarbare haka ba.   PDP ta bayyana cewa shugaban yana can zaune kuma sau 3 kacal yawa 'yan Najeriya jawabi shima sai idan an caccakeshi ne ko kuma an tuna masa cewa ya bar mutane cikin duhu basu san inda aka dosa kan yaki da cutar ba sannanne yake fitowa yay...
Buhari ya bukaci a sake yi wa fursunoni afuwa

Buhari ya bukaci a sake yi wa fursunoni afuwa

Uncategorized
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bukaci alkalin alkalan kasar ya yi wa wani adadi na fursunonin da suka shafe shekaru 6 ko fiye  da haka suna jiran shari'a a gidajen yarin kasar afuwa don dakile yaduwar annobar coronavirus.     Wata sanarwa da Reuters ta wallafa ta ruwaito shugaban Najeriyar Muhammad Buhari na umartar alkalin alkalan kasar mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad da ya rage cunkoson da gidajen yarin kasar ke fuskanta don bai wa fursunonin damar bai wa kansu kariya daga coronavirus wadda kawo yanzu ta hallaka 'yan Najeriyar 25 cikin mutum 782 da ta kama.     Sanarwar ta ruwaito shugaba Muhammadu Buhari na cewa, kashi 42 cikin 100 na fursunonin kasar dubu 74 ko fiye da haka, na zaman jiran shari'a ne dalilin da ke ci gaba da haddasa cunkos...
Bai kamata ace shugaba Buhari yayi alkawarin jagorantar yaki da Boko Haram ba>>Junaid Muhammad

Bai kamata ace shugaba Buhari yayi alkawarin jagorantar yaki da Boko Haram ba>>Junaid Muhammad

Siyasa
Daya daga cikin iyayen kasa kuma tsohon dan majalisar wakilai a jamhuriya ta 2, Junaid Muhammad ya bayyana cewa tun farko bai kamata ace shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi Alkawarin jagorantar Yakar kungiyar Boko Haram ba. Ya kara da cewa gashinan yanzu ana ta tuno mai da maganar da yayi.   A shekarar 2015 shugaban kasan, Muhammadu Buhari a Chatham House dake Landan yasha Alwashin shiga Gaba ya jagoranci yaki da Boko Haram idan aka zabeshi shugaban kasa.   "Idan aka zabeni shugaban kasa,Lamurran Najeriya ba zasu rika damun Duniya kamar yanda yake faruwa a yanzu ba, Najeriya zata dawo da karsashinta a nahiyat Africa kuma babu guri duk kankancinsa da zai kasance karkashin ikon 'yan ta'adda. Ni, Muhammadu Buhari a koda yaushe zan shiga gaba wajan ganin Najeriya ta d...