fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Muhammad Sa’ad Abubakar na III

Mun saba jin kana Allah wadai da abu idan ya faru, Mataki muke so ka dauka, ‘yan Bindiga na mulkar wasu yankunan kasarnan>>Sarkin Musulmi

Mun saba jin kana Allah wadai da abu idan ya faru, Mataki muke so ka dauka, ‘yan Bindiga na mulkar wasu yankunan kasarnan>>Sarkin Musulmi

Siyasa
Kungiyar addinin Musulunci ta Jama'atu Nasril Islam ta bayyana cewa tana Allah wadai da lamarin hare-haren da suke faruwa a Najeriya.   Kungiyar karkashin jagorancin me Alfarma, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ta fitar da sanarwa ta bakin sakatarenta, Dr. Khalid Abubakar Aliyu.   Tace Al'amarin rashin tsaro a Arewa ya ta'azzara ta yanda 'yan Bindigar sune ke saka dokoki a wasu yankuna kuma a dole jama'a ke bi dan tseratar da rayuwarsu.   Yace babu inda aka tsira, Gida, Titi ko Gona. Ya jawo hankalin shugaban kasar da ya dauki mataki ba Allah wadai ds aka saba jin yana fada ba. “Unfortunately, the common man is caught in-between two contending phenomenon; when he goes to the farm, he gets killed and when he stays at home he dies of ...
Idan ba’a saurari koken Mutane ba aka dauki mataki, Abubuwa zasu kara tabarbarewa>>Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III

Idan ba’a saurari koken Mutane ba aka dauki mataki, Abubuwa zasu kara tabarbarewa>>Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III

Siyasa
Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa idan ba'a dauki matakin sauraren koken mutane ba aka dauki matakin da ya dace, abubuwa zasu kara tabarbarewa.   Sarkin Musulmi ya bayyana hakane a wajan taron tunawa da nadin sarautar Oni of Ife karo na 5, Oba Adeyeye Ogunwusi wanda aka yi jiya, Juma'a a Ibadan.   Ya bayyana cewa taruwar sarakunan gargajiya daga kowane bangare na kasarnan a guri daya, Abin Alfaharine, musamman a irin wannan lokaci da wasu ke ta kiran a raba kasar.   Ya kuma nanata maganarsa ta matsalar tsaro a Arewa inda yace duk da shi ba dan siyasa bane amma uban 'yan siyasa ne, dan haka zai yi magana akan Siyasa, yace idan ka duba shafukan jaridu, da yawa sun dauki labarin maganar da yayi kan matsalat tsaron Arewa a A...
Ya kamata a canja yanda ake gudanar da al’amura indai ana son ci gaba a kasarnan, kuma ka yi Adalci>>Sarkin Musulmi ya gayawa shugaba Buhari

Ya kamata a canja yanda ake gudanar da al’amura indai ana son ci gaba a kasarnan, kuma ka yi Adalci>>Sarkin Musulmi ya gayawa shugaba Buhari

Siyasa
Me Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na III ya bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa indai ana son ci gaba a kasarnan sai an canja yanda al'amura ke gudana.   Ya bayyana hakane a wajan taron sarakunan gargajiya na kasa da ya faru a jiya Talata. Inda yace ya kamata shugaban kasa yayi Adalci  a dukkan lamuransa. Yace Adalci shine ginshikin zaman lafiya da ci gaba. Yace Sheikh Usman Danfodio ya fada cewa kasa zata iya dorewa da wanda basu yi imani ba amma ba zata dore da rashin adalci ba.   Ya bayyana cewa ko da a cikin gidanka ne idan babu adalci ba zaa samu zaman lafiya ba. Yace majalisarsu ta sarakuna mutanene da suka fito da bangarorin kwarewar ayyuka daban-daban tun daga Sojoji da Injiniyoyi da sauransu dan haka ba zasu ji tsoron fadar ga...
Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Kan Wawure Kayan Gwamnati, Inda Ya Ce Aikin ‘Mugunta’ Ne Kawai

Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Kan Wawure Kayan Gwamnati, Inda Ya Ce Aikin ‘Mugunta’ Ne Kawai

Siyasa
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’a Abubakar, ya bayyana wawusa da lalata dukiyar gwamnati da kadarorin gwamnati da wasu ‘yan daba suka yi a matsayin mugunta. Sarkin Musulmin wanda ya yi magana a bikin cikar Arewa House shekaru 50 a Kaduna, ya yaba wa matasan arewa kan kamun kai. Me ‘yan Nijeriya ke tunani game da wawure kayayyakin tallafi daga rumbunan adana kaya? Ya ce bai kamata a yi amfani da talauci a matsayin wani dalili na wawure dukiyar al'umma ba. Ya kara da cewa: “Mun san akwai talauci amma bai kamata a yi amfani da talauci don mugunta ba. "Saboda abin da ya faru a cikin kwanaki da suka gabata mugunta ce ta wasu mahara kuma ina ganin yana da muhimmanci a yi tir da shi da babbar murya." Ya kalubalanci shugabannin arewa da su yi aiki tukuru wajen sama...
Ya kamata a daina “Haukan da ake” a Kudancin Kaduna an mayar dashi siyasa>>Sarkin Musulmi yayi magana kan rikin Kaduna

Ya kamata a daina “Haukan da ake” a Kudancin Kaduna an mayar dashi siyasa>>Sarkin Musulmi yayi magana kan rikin Kaduna

Uncategorized
Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad III ya bayyana cewa rikicin kudancin Kaduna ya zama kamar hauka inda yayi kiran a dakatar dashi.   Sarkin ya bayyana hakane a yayin jawabin da yake a wajan taron majalisar Sarakunan Arewa da aka yi a Kaduna. Yace babu mutum mai hankali da zai rika kashe mutane da akan ko wane irin dalili ne inda yayi gargadin cewa wanda suke tada wannan rikici idan basu daina ba suma ba zasu tsira ba, zai lakume su.   Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa rikicin kudancin Kaduna ya shafe shekaru 40 ana yinsa.
Sarkin Musulmi ya umarci musulmai da su duba sabon jinjirin watan Zul-Qadah

Sarkin Musulmi ya umarci musulmai da su duba sabon jinjirin watan Zul-Qadah

Uncategorized
Mai al'farma sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya umarci al'ummar musulmi zuwa duban sabon jinjirin watan  Zul-Qadah daga ranar Lahadi, wanda yayi dai dai da 21 ga watan Yuni. Watan Dhul-Qadah shi ne wata na 11 a kalandar Musulunci wanda ke zuwa kafin watan 12 na Dhul-Hijja lokacin da al'ummar musulmi ke yin aikin hajji duk shekara. Sa'ad Abubakar ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa a ranar Asabar wacce Farfesa Sambo Junaidu, Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini, ya fitar. Inda ya sanar da cewa “Muna sanar da al'ummar musulmai cewa ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, 2020, wadda ta yi daidai da ranar 29 ga Shawwal hijira 1441 AH, ita ce ranar da za a fara duban sabon jinjirin watan  Dhul-Qadah 1441 AH. "Saboda haka, an nemi musulmai da su fara neman sa...
Wata Sabuwa: Kwayar Cutar Yunwa Tafi Illata Yan Najeriya Sama da Coronavirus A cewar Sarkin Musulmi

Wata Sabuwa: Kwayar Cutar Yunwa Tafi Illata Yan Najeriya Sama da Coronavirus A cewar Sarkin Musulmi

Kiwon Lafiya
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar II yayi Kira da gwamnati da ta dauki matakan gaggawa don inganta rayuwar 'yan Najeriya, yana mai cewa "cutar yunwa" tana kashe' yan Najeriya fiye da tsoron cutar COVID-19 (Coronavirus).   Mai alfarma Sarkin wanda ya yi jawabi a taron farko na Majalisar Addinai ta Najeriya (NIREC), a Abuja, ranar Alhamis, inda yace ko da yake, Cutar Coronavirus na kashe daruruwan mutane a fadin duniya, "   Amma a cewarsa cutar yunwa" ita ce babbar cutar da take kashe 'yan Najeriya.   Ya kuma Kara da cewa shin akwai kwayar cutar da ke kashe 'yan Najeriya da ta fi Coronavirus girma. Inda ya bayar da amsa da cewa wannan kwayar cutar itace yunwa.   A cewarsa kwayar cutar yunwa tana da matukar tsanani. Inda ya bayyana da cewa ...
A Gudanar Da Addu’o’i Kan Coronavirus>>Sarkin Musulmi

A Gudanar Da Addu’o’i Kan Coronavirus>>Sarkin Musulmi

Kiwon Lafiya
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar (Na Uku), ya bukaci da a gudanar da addu’o’i na musamman kan cutar Coronavirus, wacce ta addabi kasashe a fadin duniya.   Ya bayyana hakan ne a wata sanarwar da aka fitar wacce Sakatare Janar na kungiyar Musulunci ta Jama’atu Nasril Islam, Dr Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu a madadin sarkin.   Sarkin ya yi kira ga Musulmai da su kara mayar da hankali wajen tsaftace kansu domin hana yaduwar cutar.   A cewarsa, “hankalin mu ya tashi sakamakon ganin yadda wannan cutar ke ci gaba da yaduwa a kasashen duniya gaba daya da yadda ta ke yi wa rayukan mutane illa.”     ”A yanzu, kowace kasa na daukar matakai kamar killace mutanen da ake kyautata zaton sun kamu da cutar...