fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Muhammad Sanusi II

Tunda an baka Khalifan Tijjaniyya, yanzu kana da damar hana Bara da Almajirci>>’Yan Arewa ga Sarki Sanusi

Tunda an baka Khalifan Tijjaniyya, yanzu kana da damar hana Bara da Almajirci>>’Yan Arewa ga Sarki Sanusi

Siyasa
A jiya ne dai aka samu Rahotannin cewa an nada tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyya na Najeriya.   Bayan Nadin, Wasu 'yan Arewa sun hau shafukan sada zumunta inda suka rika kira a gareshi da yayi kokarin ganin an hana Almajirci da kuma bara.   Sun rika tuna masa cewa, a baya ya sha kira da a daina Bara da almajiranci, to yanzu ga dama ta samu a gareshi da zai yi a aikace.   Wani me suna Abubakar Hadimi ya bayyana cewa, shugabancin Tijjaniyya da Sarki Sanusi ya samu, damace Allah ya bashi ta kawo karshen Almajiranci a aikace. Ya bayyana cewa, kusan duka Almajirai ko dai 'yan Qadiriyya ko Tijjaniyya ne. Yace yana fatan zai kira iyayen wadanna yara dan su kwashesu daga kan tituna.   Ya kara da cewa, ci gaba da ma...
An nada tsohon Sarkin Kano:Muhammad Sanusi II, Khalifan Tijjaniyya a Najeriya

An nada tsohon Sarkin Kano:Muhammad Sanusi II, Khalifan Tijjaniyya a Najeriya

Siyasa
An nada tsohon Sarkin Kano Sanusi II Khalifan Tijjaniya a Najeriya An naɗa tsohon sarkin Kano Sanusi na II a matsayin jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya. Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoraci naɗa tsohon sarkin a matsayin Khalifa a babban taron ɗariƙar da aka gudanar a jihar Sakkwato. Sarki Sanusi na II yanzu ya gaji kakansa Khalifan Tijjaniya na farko a Najeriya. Tun mutuwar marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu ba a naɗa sabon Khalifa ba a Najeriya. Taron ya samu halartar manyan shugabannin ɗarikar Tijjaniya na Najeriya da wajen ƙasar da suka haɗa babban malami Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Gwamna El-Rufai ya baiwa tsohon Sarkin Kano, Sanusi II mukami a hukumar KADIPA ta Jihar Kaduna

Gwamna El-Rufai ya baiwa tsohon Sarkin Kano, Sanusi II mukami a hukumar KADIPA ta Jihar Kaduna

Siyasa, Uncategorized
Gwamna Nasir El-Rufai ya nada tsohon Sarkin Masarautar Kano, Mohammed Sanusi, a matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar Raya Jarin Kasuwancin Kaduna (KADIPA). El-Rufai ya kuma umarci hukumar da ta ninka kokarin ta na sanya jihar a sahun gaba a duk fadin Najeriya, ta hanyar inganta matsayin saukaka harkokin kasuwanci. El-Rufai, wanda yayi magana a wajen bikin kaddamar da hukumar, ya yiwa Sanusi II maraba a hukumance. Ya kuma godewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, bisa karban hidimtawa mutanen jihar Kaduna. El-Rufa'i ya ce hukumar ta kasance muhimmiyar hanya kuma mai nasara a harkar saka jari a Kaduna, kuma ta fitar da sama da dala biliyan 2.1 a zahiri. El Rufa'i ya ci gaba da cewa KADIPA za ta yi takara ba kawai tare da sauran jihohin Nijeriya don saka hannun...
Bababar matsalata da Sarki Sanusi da har tasa na tsigeshi daga Sarauta shine surutunsa yayi yawa, yana caccakar Gwamnati>Gwamna Ganduje

Bababar matsalata da Sarki Sanusi da har tasa na tsigeshi daga Sarauta shine surutunsa yayi yawa, yana caccakar Gwamnati>Gwamna Ganduje

Siyasa
Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa dalilin da yasa ya sauke Sarki Sanusi daga Sarauta shine satkin bai san aikin da ya kamata a ce sarki na yi ba.   Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channelstv.  Yace sarki Sanusi ya rika kawo abubuwan da zasu lalata masarautar Kano dake da mutunci a idanun jama'a.   Yace Sarki Sanusi tsohon me sukar gwamnati ne amma da ya zama sarki sai ya kasa canjawa daga yawan surutun da yake zuwa irin halayyar da aka san sarki da ita.   Gwamna Gwamna Ganduje yace wannan itace babbar matsalar da ya samu da Sarki Sanusi shiyasa ya saukeshi. “The real story was that the deposed emir of Kano did not understand the responsibilities of a traditional ruler especially for a strong institution like t...
Ban nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano don na bata wa Jonathan rai ba>>Kwankwaso

Ban nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano don na bata wa Jonathan rai ba>>Kwankwaso

Siyasa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya musanta nada wani tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano don ya batawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan rai.   Kwankwaso ya mayar da martani ne ga kalaman da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje yayi inda yace Kwankwaso ya nada Sanusi II don ya batawa tsohon shugaban kasa Jonathan rai. A lokacin da yake gabatar da wani littafi a kan Jonathan, Ganduje ya ce Sanusi ba shi ne mutumin da ya fi dacewa da gadon sarauta ba a lokacin da aka nada shi a watan Yunin 2014, yana mai cewa an nada Sarkin da aka tsige ne domin ya batawa tsohon Shugaban kasar rai.   Gwamnan ya kuma ce an cire Sanusi daga mukaminsa domin ya ceci tsarin da kuma cibiyoyin gargajiya.   Duk da ...
Hotuna:Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sausi II ya kara samun wani babban Mukami

Hotuna:Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sausi II ya kara samun wani babban Mukami

Siyasa
Tsohon Sarkin Kano,  Muhammad Sausi na II ya samu takardar data tabbatar masa zama shugaban jami'ar Jihar Ekiti.   Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya baiwa Sarki Sanusi wannan mukami na VC. A ranar 17 ga watan Disamba aka mikawa Sarki Sanusi takardar nadin da aka masa sannan kuma ya jagoranci taron yaye daliban jihar. HH Muhammad Sanusi II officially accepted his appointment letter as the Chancellor of Ekiti State University as appointed H.E Governor Kayode Fayemi. His Highness also presided over the 24th Convocation of Ceremonies as the Chancellor of the University. 17th, Dec 2020.  
Da aka saukeni daga Sarki ban yi tunanin zuwa Kaduna, Sokoto ko Maiduguri ba, Legas nace zanje>>Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II

Da aka saukeni daga Sarki ban yi tunanin zuwa Kaduna, Sokoto ko Maiduguri ba, Legas nace zanje>>Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II

Siyasa
Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa da aka saukeshi daga Sarautar Kano bai ce zai je Kaduna, Sokoto ko Maiduguri ba, yace Legas yaso zuwa amma aka hanashi aka kaishi can wani gari a Nasarawa.   Yace jirgin dake Filin Jirgin sama yana jiransa, na wani abokinsa ne daga kudu. Sannan kuma haka aka dauki iyalinsa aka kaisu Legas, Abokansa suka basu wajan zama aka baau Abinci. Yace bayan da ya koma Legas, shima ya kwana biyu a inda aka sauke Iyalan nasa, daga baya abokansa suka gyara masa gidan da ya siya a Legas din tun yana aikin banki ya koma.   Yacs to a haka ta yaya za'a gaya masa cewa Kiristoci ko kuma mutanen kudu ba mutanen kirki bane? Da yake ci gaba da magana, Sarkin Yace kuma da mahaifinsa bai kaishi makaranta ba, da zai zama abinda ya zama a y...
Dalilin da ya sa na sauke Sanusi a matsayin Sarkin Kano>>Gwamna Ganduje yayi bayani Dalla-Dalla

Dalilin da ya sa na sauke Sanusi a matsayin Sarkin Kano>>Gwamna Ganduje yayi bayani Dalla-Dalla

Siyasa
Dalilin da ya sa na sauke Sanusi a matsayin Sarkin Kano - Gwamna Ganduje Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje a ranar Talata ya bayar da dalilan da suka sa ya tsige Alhaji Muhammadu Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano.   Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne domin ya ceci tsarin masarautar gargajiyar daga cin zarafi.   Gwamna Ganduje yayi magana ne yayin gabatar da wani littafi kan tsohon shugaban kasa Goodluck Johnathan, wanda wani dan jarida, Bonaventure Philips Melah ya rubuta.   A cewarsa, Sanusi ba shi ne mutumin da ya fi dacewa da gadon sarauta ba a lokacin da aka nada shi a watan Yunin 2014, yana mai cewa an nada Sarkin da aka tsige ne domin kawai a bata wa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan rai.   Jonathan ya kasance a watan Afril...