Tsohon sarkon Kano, Muhammad Sanusi II ya sake kai ziyara jihar Kaduna daga Legas.
Sarki Sanusi ya shiga Kadunane da yammacin Jiya, Juma'a.
https://twitter.com/MSII_dynasty/status/1311998394118930433?s=19
Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa yana goyon bayan cire tallafin Man Fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Sarki Sanusi ya bayyana hakane a wajan Wani Taro da ya halarta da aka yi saboda cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai.
Sanusi ya bayyana cewa shuwagabannin siyasa yawanci ba wakiltar Mutanensu suke ba, aljihunansu suka sani.
Ya baiwa mutane shawarar cewa su rika su lura, ba wai sai Mutum na siyasane yake wakiltar mutanensa ba.
Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa yawancin masu fafutukar kare 'yancin yankunan kasarnan ba wai da gaske suke ba.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN ya bayyana hakane a wajan wani shiri da CCC ta shirya a Legas wanda aka yishi dan murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai.
Yace idan ka duba zaka ga tunda aka kafa Najeriya duk gwamnatin da ta zo sai da baiwa mutane daga kowane yanki na kasarnan mukami. Yace dan haka yawancin masu rike da mukaman siyasa Aljihunan su suka sani.
Yace ya kamata mutane su gane cewa ba wai sai kana rike da mukamin siyasa bane sannan zaka iya wakiltar jama'ar ka ba.
Ya kuma yabawa gwamnati bisa cure tallafin man fetur da ta yi.
Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya katbi bakuncin sarkin Muri a gidansa dake Kaduna, Jiya, Laraba a yayin da ya kai masa ziyarar ban girma.
https://twitter.com/MSII_dynasty/status/1308825779229413376?s=19
Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa babban dalilin da yasa mutane basu gamsu da karin kudin wuta ba shine saboda yawanci babu wani harkar samu da suke da ita.
Yace ita kanta gwamnatin tana kallon wutarne a matsayin fanin 'yan kasa kawai, bawai yanda zasu amfana da wutar ta fannin karuwar tattalin arzikin su ba.
Yace misali idan kaje kauye ka kara kudin wuta amma mutum na samun kudi daga amfani da wutar da suka nunka kudin da zai biya har sau 4, yace na zai yi wata-wata ba zai biya kudin wutar.
Yace amma mafi yawancin mutane basa amfana da wutar ta wajan habakar tattalin arzikinsu dan haka suka ki amincewa da karin kudin wutar. Ya bayyana hakane a wajan taron tattalin arziki a Kaduna wanda Channelstv ta ruwaito.
Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa idan aka kwatanta ci gaban Najeriya da wasu kasashen yankin Asia za'a cewa har yanzu Najeriya na nan inda take ba ta ke ko ina ba.
Sarkin ya bayyana haka ne wajan taron tattalin arziki dake gudana a jihar Kaduna inda ya bayar da jawabi ta gidan Talabijin din Channelstv.
Ya kuma bayyana cewa kamata yayi a koyawa matasa sana'o'i ta yanda zasu dogara da kansu, bawai kawai du rika amfani da wayoyinsu suna shigowa da kaya daga kasashen waje ba.
Yace idan matasa suka zama masu hazaka da kirkira to ba zama su damu da saka ido a harkar gwamnati ba
Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II Ya Jagoranci Zikirin Juma'a A Birnin Landan
Mai Martaba Muhammadu Sunusi II kenan a da'irar zikirin Juma'a a Zawiyyar Rumis Cafe dake birnin London a ƙasar Ingila.
Allah ya karawa Muhammadu Sunusi lafiya da daukaka ya saka masa da alkairi. Amin.
Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana rashin Adalci na tsare-tsaren gasar masana'antu na Cibiyar kasuwancin Duniya a matsayin abinda ya kashe masana'antun Arewa.
A baya Arewa ta zama abin ban sha'awa inda masanaantu da dama suke ta gudana. Allah jikan Sir Ahmadu Bello, Sardauna, Firimiyan Arewa, yayi kokarin ganin an kafa masana'antu da dama a Arewa kuma kamin rasuwarsa Burinshi ya cika.
Masakun dake Arewa a wancan lokacin sune na 2 wajan samawa al'umma aiki bayan gwamnati sannan manya-manyan kamfanonin Duniya duk kusan suna da rassa a Arewa, irinsu Peugeot, Mandilas, UTC, NASCO, UAC, Kingsway, Leventis, Yamaco dadai sauransu. Kamin daga baya su kulle su bar yankin.
A wancan lokacin Mutanen Kauyuka ba kasafai suka damu da zuwa cirani Birni ba ko...
Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa burinsa yanzu shine ya fara rubuce-rubuce dan ya samu Giri na digirgir watau,PhD.
Yace sannan kuma zai ci gaba da bincike da rubuce-rubuce har ya zama farfesa saboda yana son komawa tsohuwar sana'arsa ta koyarwa a jami'a amma a wannan karin a kasashen turai.
Sarkin ya bayyana hakane a hirar da Arise TV ta yi dashi inda yaci gana da cewa idan ya zama Farfesa da wuya a samu mutum kamarsa, wanda ya taba zama shugaban bankin kasuwanci sannan ya zama gwamnan babban bankin Najeriya sannan ya zama sarki sannan kuma Farfesa. Yace da wannan nasarori babu jami'ar Duniya ko Harvard ko ma wacce da ba zata daukeshi aiki ba.
A jiya dai Tuni Me martaba har ya isa kasar Ingila inda ake sa ran zai fara aiki dan ci...
Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II kenan a wadanan hotunan yayin da yake a gidansa dake Oxford kasar Ingila.
A baya dai mun kawo muku cewa sarkin ya bayyana son yin wasu rubuce-rubuce da zasu sa ya samu Digiri na PhD da kuma zama Farfesa a karshe.
https://twitter.com/MSII_dynasty/status/1302389841225756672?s=19