
Ba Ni Da Burin Tsayawa Takara A Zaben 2023>>Tsohon Sarkin Kano Muhammdu Sanusi II
Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II ya ce ba shi da burin takarar kujerar siyasa. Burinsa shine komawa karantarwa kamar yadda ya fara a farkon rayuwarsa kafin ya zama ma'aikacin banki.
A wata tattaunawa da tsohon Sarkin ya yi da Arise TV a yau Juma'a, ya ce ba shi da ra'ayin siyasa kwata-kwata.
Tsohon Sarkin ya ce zai koma karatu a fitacciyar jami'ar Oxford da ke Ingila a watan Oktoba mai zuwa. Hukumar kwamitin cibiyar Afrika ta makarantar, ta amince da bukatar Sanusi na komawa karatu a can.