fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Tag: Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga Masarautar Katsina bayan Sarkin Sullubawa Hakimin karamar hukumar Kaita ya rasu

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga Masarautar Katsina bayan Sarkin Sullubawa Hakimin karamar hukumar Kaita ya rasu

Breaking News
Shugaba Muhammdu Buhari ya mika sakon ta'aziyarsa ga masauratar Katsina biyo bayan rasuwar hakimin karamar hukumar Kaita, Sarkin Sullubawa Abdulkarim Usman. Marigayi ya kasance kanin mai martaba sarkin Katsina Abdulmumin Usman kuma wa ga darektan kudi na jihar Abuja, Kabiru Hassan. A wasikar data fito daga hannun maitaimakin mai lura da kafafen sata zumunta na shugaba Buhari, Garba Shehu wacce sanata Hadi Siraka ya jagoranci kaiwa ta msarauta ta bayyana cewa, "A matsayina na shugaban Kasa da kuma Al'umma baki daya muna mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan arziki na marigayi sarkin Sullubawa Allah ya rahamshe shi".  
Shugaba Muhammadu Buhari yayi maraba da zuwan Ramadan, inda ya bukaci musulmai dasu ciyar da marasa karfi

Shugaba Muhammadu Buhari yayi maraba da zuwan Ramadan, inda ya bukaci musulmai dasu ciyar da marasa karfi

Breaking News
Shugaban kasar Najeriya, mejo janar Muhammadu Buhari yayi maraba da zuwan watan Ramadan mai dumbin daraja da alfarma. Ramadan ya kasance wata mai alfarma kuma mai albarka wanda musulmai suke azumta, kuma yana kara masu kusance da tsron mahaliccin su wato Allahu Subhanahu Wata'ala. Inda shima Shugaba Buhari ya taya yan uwa musulmai na fadin duniya murnar shiga watan mai alfarma, kuma ya bukaci musulmai masu arziki cewa suyi kokari wurin ciyar da marasa karfi a wannan watan mai albarka.
Muhammadu Buhari ya taya Tinubu murnar cika shekara 70

Muhammadu Buhari ya taya Tinubu murnar cika shekara 70

Siyasa
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari tare da sauran shuwagabanni da kuma membobin APC sun taya tsohon gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu murnar cika shekara 70. Mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawarwari ta fannin kafafen sada zumunta, Femi Adisina ne ya bayyana hakan ranar litinin. Inda yace shugana Buhari ya yabi Tinubu sosai bisa namijin kokarin dayake yi a jam'iyyar APC, kuma yayi mai addu'a Allah ya kara mai lafiya da misan kwana.
“Abokan adawa sunji kunya domin mun gudanar da taro cikin limana”:Muhammadu Buhari

“Abokan adawa sunji kunya domin mun gudanar da taro cikin limana”:Muhammadu Buhari

Breaking News, Siyasa, Uncategorized
Shugaban kasar Najeriya mejo janar Muhammadu Buhari ya taya sabon shugaban APC Addullahi Adamu da sauran yan kwamitin jam'iyyar murna bayan sun gudanar da babban taro ranar asabar. Buhari ya mika sakon ne a ranar lahadi inda yace yaga alamun nasara a tattare da jam'iyyar saboda hadn kan da suka bayar, wanda ke nuna cewa sune zasu lashe zaben shekarar 2023. Shugaban ya kara da cewa abokan adawarsu masu son tada zaune tsaya wato PDP sunji kunya saboda sun gudanar da taron cikin limana.
Kungiyar SERAP ta baiwa shugaba Buhari mako guda yayi bincike akan yadda akayi tiriliyan 11 ta wutar lantarki ta sulwanta

Kungiyar SERAP ta baiwa shugaba Buhari mako guda yayi bincike akan yadda akayi tiriliyan 11 ta wutar lantarki ta sulwanta

Breaking News, Tsaro
Kungiyar SERAP me fafutukar yaki da cin hanci da kuma kare hankin bil'adama ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari mako guda yayi bincike akan hadda akayi naira tiriliyan 11 ta wutar lantarkin Najeriya ta sulwanta. Inda kungiyar ta bukaci Muhammadu Buhari daya umarci ministan Shari'a Abubakar Malami da sauran jami'an dake yaki da cin hanci da suyi bincike akan yadda aka yi da kudaden tun daga shekarar 1999. Kuma ta kara da cewa idan ba'a dauki matakai bato nan da shekaru goma za'a iya yin asarar naira tiriliyan 20.  
Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Landan

Breaking News, Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya inda ya sauka a babban birni  tarayya Abuja da misalin karfe bakwai na yamma. Buhari ya dawo ne daga Landan bayan ya kammala gwajin lafiyarsa. Shugaba ya bar kasa Najeriya ne a ranar shida ga watan maris kuma dama makonni biyu yace zaiyi kafin ya dawo, kuma yanzu ya sauka cikin koshin lafiya.
“Ina baku hakuri akan karancin man fetur da rashin wutar lantarki”>> Buhari ya fadawa yan Najeriya daga Landan

“Ina baku hakuri akan karancin man fetur da rashin wutar lantarki”>> Buhari ya fadawa yan Najeriya daga Landan

Uncategorized
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa akan mawuyacin halin da Najeriya ke ciki na rashin man fetur da kuma wutar lantarki. Inda yasha alwashin cewa nan bada dadewa ba komai zai daidaita domin gwamnati na iya bakin kokarinta akan lamarin. Kuma shugaban kasar ya bayar da hakuri akan lalataccen man fetur din da aka shigo dashi kasar wan ya hallaka injina da kuma ababen hawa. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne daga Landan inda yayi tafiyar domin duba lafiyarsa.
“Kubar Mala Buni ya cigaba da jan ragamar jam’iyyar APC”>> Shugana Buhari

“Kubar Mala Buni ya cigaba da jan ragamar jam’iyyar APC”>> Shugana Buhari

Siyasa
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a bar gwamnan jihar Yobe Mala Buni ya cigaba da jan ragamar al'amuran jam'iyyar APC. Gwamnan jihar Niger Abubakar Bello ne ya cigaba da jan ragamar al'amuran APC bayan jam'iyyar ta cire kwace matsayin daga hannun Mala Buni. Amma kungiyar zabe ta INEC tayi watsi da sakon da Bello ya tura mata na taron da APC keso ta gudanar, inda kungiyar ta bayyana cewa ita Mala Buni ta sani a matsayin mai jan ragamar jam'iyyar APC ba Bello ba.
Kungiyar SERAP ta maka shugaba Muhammadu Buhari Buhari a kotu tare da Mr. Aliyu Fantami

Kungiyar SERAP ta maka shugaba Muhammadu Buhari Buhari a kotu tare da Mr. Aliyu Fantami

Uncategorized
Kungiyar SERAP ta maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu akan damar daya baiwa hukuma na sanin sirrin kiran waya ta hanyar hada layin waya da katin dan kasa. A watan fabrairu ne shugaba Buhari ya baiwa hukuma damar sanin bayanan yan Najeriyan wurin gudanar da ayyukan su. Amma yanzu kungiyar SERAP ta bukaci babbar kotu dake jihar Legas cewa tayi bincike akan wannan lamarin sosai domin ya sabama kundin tsarin mulki na shekarar 1999. Bayan shugaban kasa, kungiyar kare hakkin bin'adaman ta maka Mr Abubakar Malami, ministan shari'a Attorney da kuma Mr Isa Pantami ministan sadarwa duk a kotu.