fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Tag: Muhammadu Buhari

Yau Kwanan Baba 25 Cif Bai Hau Jirgi Zuwa Kowacce Kasa Ba

Siyasa
Allah ya sa Baban ya yi amfani da wadannan kwanaki da muka yi tare da shi a cikin kasa, ta yadda zai yi duba zuwa ga matsalolin talakawan da yake mulka.   Shi ya sa muke amfani da wannan dama ta hanyar tura korafe-korafen mu gare shi, duba da cewa yana nan bai je ko ina ba.   Mun gode Allah da samun wannan dama. Allah Ya raba qasar mu da annobar cutar CORONA-VIRUS, ta yadda zamu zauna cikin aminci mu da Shugabannin mu, wala'alla sa fahimci matsalolinmu. Mubarak.
Fadar shugaban kasa ta bayyana shirin Buhari ga kabilar Igbo

Fadar shugaban kasa ta bayyana shirin Buhari ga kabilar Igbo

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa zai kammala ayyukan ci gaba a yankin Kudu Maso Gabashin kasar kafin karewar mulkinsa a shekarar 2023. Mai ba shi shawara na musamman kan harkar yada labarai, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, lokacin da ya karbi  Editocin jaridar Orient Daily Newspaper, karkashin Editan Stanley Egbochuku.  Adesina ya ce ana ci gaba da aiwatar da ayyukan gwamnatin tarayya da yawa a cikin jihohi biyar na kudu maso gabashin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo. Ya ba da labarin cewa, a cikin shekara ta 2018, Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ya lissafa ayyukan ci gaba 69 a yankin kudu maso gabas, inda ya bayyana galibi hanyoyi ne da gadoji. Adesina ya yi maraba da wannan yunƙurin da ƙungiyar kafofin w...
Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin Kaduna inda ya jajantawa wanda lamarin ya rutsa dasu

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin Kaduna inda ya jajantawa wanda lamarin ya rutsa dasu

Siyasa, Uncategorized
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da harin da 'yan bindiga suka kai jihar Kaduna da ya kashe mutane da dama a Ranar Lahadin data gabata. Wannan na kunshene a cikin wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar,Malam Garba Shehu ya fitar ga manema labarai. Shugaban yace a bayyane yake wannan hari da 'yan bindigar suka kai suna nuna fushinsu ne akan mutanen da basu ji basu gani ba saboda matsa musu da hare-hare da jami'an tsaro suka yi a dazukan Birnin Gwari fa Kaduru. Yace babu wani abu da 'yan bindigar za su yi da zai hana gwamnati murkushe su dan kiwa ba zasu rika kaiwa mutane hari ba tare da an murkushesu ba. Shugaban ya jajantawa wanda lamarin ya rutsa dadu inda kuma ya baiwa gaba dayan 'yan Najeriya tabbacin cewa gwamnati zata dukufa dan ganin ta kawo kars...
Ku Kwantar Da Hankalinku, Kada Ku Tsorata Da Cutar Corona Virus>>Shugaba Buhari Ga ‘Yan Nijeriya

Ku Kwantar Da Hankalinku, Kada Ku Tsorata Da Cutar Corona Virus>>Shugaba Buhari Ga ‘Yan Nijeriya

Siyasa
Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da sanarwa cewa, ya yi kira ga kowa ya kwantar da hankalin sa, dangane da bullar cutar Coronavirus. PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin bullar cutar a karon farko a Lagos, bayan da wani Baturen kasar Italiya ya shigo cikin kasar nan dauke da cutar. Tun bayan killace shi da aka yi a Lagos da sauran jihohi da dama suka fara daukar kwararan matakan yin kaffa-kaffa, ta hanyar wayar da kan jama’a dangane da matakan kariya ko gujewa ga kamuwa da cutar. An kuma bada labarin killace wasu ‘yan China su uku, a jihar Filato, tare da wasu ‘yan Najeriya su 39 da ke wa ‘yan Chana din aikin hakar ma’adinai. A jihar Cross River gwamnatin jihar ta dukufa wajen yin amfani da shela da kuma cikin coci-coci ta na fadakar da jama’a cikin yare daban-daban. ...

“Ya Allah kada kayi watsi da lamurranmu kamar yanda Shugaba Buhari yayi watsi da lamurran gwamna Fayose”>>inji wani bawan Allah

Uncategorized
A jiyane gwamnan jihar Ekiti Ayodele fayose yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi, a cikin maganganun da yayi yace yayi fatan ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tayashi murnar zagayowar ranar haihuwar tashi, wani bawan Allah da yake bibiyar lamurran gwamnan yace yana fatan kada Allah ya yayi watsi da lamuran mu kamar yanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi watsi da gwamnan duk da kokarin babatun da yake yi na ganin ya tsokani sugban. Matashin dai yayi rubutu a dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter akan gwamnan, da ya dauki hankulan mutane da yawa kamar haka:  Lallai Shugaba Buhari ya cika mutum me dattako, Gwamna Fayose ya shafe shekaru biyu da rabi yana ta tsokanarshi amma baba( Buhari yayi watsi dashi kamar bai san Allah yayi ruwan tsirarshiba...

Shugaba Buhari yakai ziyarar aiki jihar Ebonyi: An bashi sarautar “Abokin kowa: Ya bude wata katafariyar gadar sama

Uncategorized
A yau Talatane shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara wata ziyarar kwanaki biyu a jihar Ebonyi, jirgin saman shugaban kasar ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa me suna Akanu Ibiam dake jihar Enugu inda gwamnonin jihohin Enugu da Ebonyi da Imo da Kogi da kuma tarin jama'a suka suka tarbeshi. Daga nan shugaban kasar ya zarce zuwa Ebonyi inda nanne zai fara ziyarar kafin gobe ya wuce Anambra . An baiwa shugaban kasar wata sarautar gargajiya me suna Enyioma 1 of Ebonyi, wadda rahotanni suka bayyana cewa tana nufin Abokin kowa, wasu kuma sun fassara sarautar da cewa tana nufin abokin mutanen Ebonyi. Shugaban kasar ya bude wata katafariyar gadar sama da aka gina a jihar ta Ebonyi, haka kuma an bashi kyautar goro, gobene ake saran zai wuce jihar Anambra ifan Allah ya kaimu. ...

Buhari Ya Marawa El Rufa’i Baya Kan Shirin Korar Malamai 21, 780

Uncategorized
Shugaba Muhammad Buhari ya marawa Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i baya kan shirinsa na korar malaman makarantar Firamare har 21, 780 wadanda suka kasa cikin wata jarrabawar gwajin cancanta da aka shirya masu. Da yake jawabi a wurin taron karawa juna sani da aka shiryawa ministoci Shugaba Buhari ya nuna damuwa kan yadda bangaren ilimin ya tabarbare inda ya yi alwashin ganin cewa gwamnatinsa ta farfado da darajar ilimin. Shugaba Buhari ya bayar da misali da wani mutum wanda ya ki bayyana sunansa wanda ya shaida masa a shekaru goma da suka wuce inda ya ziyarci makarantar Firamaren da ya kammala don ya bayar da tasa gudunmawa amma abin mamaki sai ya kasa rabe tsakanin dalibai da malaman makarantar. A cewar Buhari abin da mutumin nan ya shaida masa shi ne El Rufa'i ke son aiwata...
An yiwa shugaba Buhari addu’o’in samun lafiya a kasashen Ingila da Gini

An yiwa shugaba Buhari addu’o’in samun lafiya a kasashen Ingila da Gini

Uncategorized
Al'ummar Musulmin kasar Guinea Conakry sun yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari addu'o'in fatan samun sauki a masallatan Juma'an kasar. A ranar Laraba ne Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya ba da umurnin gudanar da addu'o'in, a lokacin taron majalisar ministoci. Shugaba Alpha Conde shi ne shugaban Tarayyar Afirka. Hakazalika, kungiyar Musulmin Najeriya a Birtaniya ta gudanar da addu'o'in rokon samun lafiyar Shugaba Buhari wanda yake jinya a Landan fiye da wata biyu a ke nan . A watan Maris da ya gabata ne aka tsara shugaba Buharin, zai kai ziyara Guinea, amma sai aka dage tafiyar tasa. bbchausa.