fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Tag: mulki

Zamu zauna da shugaba Buhari,Obasanjo, Atiku da Tinubu dan tattauna yanda za’a bamu mulki a 2023>>Kungiyar kare muradun Inyamurai

Zamu zauna da shugaba Buhari,Obasanjo, Atiku da Tinubu dan tattauna yanda za’a bamu mulki a 2023>>Kungiyar kare muradun Inyamurai

Siyasa
Kungiyar matasa masu kare muradun Inyamurai me sunan OYC ta bayyana cewa tuni ta fara shirye-shiryen ganin cewa dan kabilar ya dare kan mulkin shugabancin kasarnan a shekarar 2023.   Tace tana jirane a gama da matsalar Coronavirus/COVID-19 dan ta fara aiki haikan wajan ganin burinta ya cika.   Kungiyar tace zata zauna da shugaban kasa,Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da Tsohon shugaban kasa,Olusegun Obasanjo da kuma jiho a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu dan su tattauna batun.   Sun kara da cewa hana wani bangare mulki a kasarnan yana da matsala dan kuwa idan aka ce ba za'a basu mulki ba to maganar neman kafa kasarsu ta Biafra zata ci gaba, hakanan suma Yarbawa tabbas zasu ci gaba da neman kafa kasar Oduduwa. ...

Gwamnan jihar Kaduna ya zama abin koyi ga sauran gwamnonin kasarnan akan gyaran Ilimi

Uncategorized
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya zama abin koyi ga sauran gwamnonin jihohin kasarnan musamman Arewa, akan yiwan malaman firaimare jarabawa da kuma tantance wadanda suka cancanta sannan a sallami wadanda basu cancantaba. Kwanannan ne gwamnan ya shiryawa malaman firaimare na jihar jarabawar ' yan aji hudu amma sakamakon jarabawar ya nuna cewa guda dubu ashirin da biyu sun fadi kuma gwamnan zai sallamesu aiki ya dauki wasu sabbin malam su dubu ashirin da biyar. Wannan batu ya dauki hankulan mutane sosai inda wasu dake tausayawa malaman da za'a kora suka bayyana cewa bai kamata a koresuba, kamata yayi a basu horaswa ta musamman ko kuma a mayar dasu wata ma'aikatar inda ba zasuyi koyarwa ba, tunda ba dadi mutum da iyali a kulle mishi hanyar samu. Wasu kuma sun bayyana cewa t...

Buhari Ya Marawa El Rufa’i Baya Kan Shirin Korar Malamai 21, 780

Uncategorized
Shugaba Muhammad Buhari ya marawa Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i baya kan shirinsa na korar malaman makarantar Firamare har 21, 780 wadanda suka kasa cikin wata jarrabawar gwajin cancanta da aka shirya masu. Da yake jawabi a wurin taron karawa juna sani da aka shiryawa ministoci Shugaba Buhari ya nuna damuwa kan yadda bangaren ilimin ya tabarbare inda ya yi alwashin ganin cewa gwamnatinsa ta farfado da darajar ilimin. Shugaba Buhari ya bayar da misali da wani mutum wanda ya ki bayyana sunansa wanda ya shaida masa a shekaru goma da suka wuce inda ya ziyarci makarantar Firamaren da ya kammala don ya bayar da tasa gudunmawa amma abin mamaki sai ya kasa rabe tsakanin dalibai da malaman makarantar. A cewar Buhari abin da mutumin nan ya shaida masa shi ne El Rufa'i ke son aiwata...

“Mutane har daga Arewa nata damuna in sake tsayawa takarar shugaban kasa”>>Goodluck Jonathan

Uncategorized
Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa yana ta samun jama'a na ziyartarshi daga sassa daban-daban na kasarnan suna rokonshi ya sake tsayawa takara, ya kara da cewa abinda yafi taba mai zuciya shine idan ya shiga taron Jama'a zakaji mutane nata shewar ka dawo goodluck! Ka dawo goodluck, yace irin wannan yana sashi ya zubar da hawaye. Ya bayyana hakane lokacin da yake hira da sanannen da jaridarnan Dele Momodu amma ya kara da cewa maimakon yaji wani matsayi da girman kai ya shigeshi a duk lokacin da irin haka ta faru yakan tuna irin kurakuran da ya yayi a baya sai yaji bai kamata yayi dagawa ba. Ya kara da cewa bai san abin da Allah ya boye ba amma gaskiya akwai matukar wuyar gaske ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan, ya bayar da iya gudumuwarshi, za...

Kalaman Sanata Shehu Sani akan korar malaman jihar Kaduna daga aiki sun jawo cece-kuce

Uncategorized
 Sanata Shehu Sani me wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar tarayya yayi wasu rubuce-rubuce da suka dauki hankulan mutane suka kuma jawo cece-kuce a dandalinshi na sada zumunta da muhawara da shafin Twitter. Sanatan yayi maganane akan batun da wata kididdiga da akayi ta nuna cewa 'yan sandan Najeriyane na daya a Duniya wajan rashin yin aiki yanda ya kamata, sanatan yace wasu zasu iya cewa a kori 'yan sandanmu daga aiki tunda ance basu iya aikiba, ban yarda da irin wannan ra'ayiba. Duka da dai sanatan be kama suna ba amma mutane da yawa sun fahimci cewa da gwamnan jihar Kaduna yake akan batun sallamar malamai da yace zaiyi bayan da aka musu jarabawar 'yan aji hudu mafi yawanci su suka kasa cin jarabawar. Masu sharhi da damane suka bayyana cewa be kamata sanata Shehhu Sani ya ...