fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Muller

Dan wasa 1 bazai iya tare Messi ba>>Muller

Dan wasa 1 bazai iya tare Messi ba>>Muller

Wasanni
Thomas Muller ya bayyana cewa kungiyar shi ta Bayern Munich sai ta dage sosai a wasan da zasu buga anjima da kungiyar Barcelona domin su dakatar da Messi. Kaftin din Barcelonan shine ya jagoranci abokan aikin shi yayin da suka yi nasarar cire Napoli a gasar ta Champions League. Muller yayi jawabi akan wasan da zasu buga anjiman yayin da yake cewa, Muhimmiyar maganar da zai yi itace Messi ba irin yan wasan da ake dakatarwa bane da dan wasa guda. kuma a fahimtar shi idan har za'a dakatar da Messi to sai dai a kungiyance ta yadda idan ya wuce dan wasa na farko sai na biyu yazo shima idan ya wuce shi sai na uku yazo sannan kuma sauran yan wasan guda biyu su kara komawa bayan shi. Ya kara da cewa ba zai yiyu a dakatar da Messi da dan wasa daya ba saboda haka ya kamata su dage....