
Kungiyar kare muradin musulmai (MURIC) ta aike da sakon ta’aziyya zuwa ga mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar III, bisa rasuwar dan uwansa
Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) ta jajantawa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar III, bisa rasuwar dan uwansa, Alhaji Abdulkadir Abubakar.
Farfesa Ishaq Akintola, Daraktan kungiyar shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jihar Legas a ranar Lahadi, inda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kwazo.
Yayi Addu'ar Allah ubangiji ya gafarta masa ya kuma sanya Al'janna makoma.