
Wal iyazu Billah:An gano wani sabon Mummunan cin Zarafi da kasar China ke wa Musulman kasar
An gabo wani sabon cin Zarafin da kasar China kewa Musulman Uighur dake yankin Xinjiang na kasar.
Kasar tana tilastawa Musulman zuwa gona da yin aikin gyaran auduga da hannunsu ba tare da kariya ba.
Yawan musulman da aka saka a wannan aiki sun kai akalla rabin Miliyan. A shekarar 2018 ma an samu irin wannan Rahoto inda mutane 570,000 daga yankin aka aikasu aikin cinkar audugar ta hanyar tursasawa.
Yankin Xinjiang shin yankin da yafi kowane a Duniya samar da auduga Wanda ke samar da kashe 20 cikin 100 na audugar da ake amfani da ita a Duniya.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun bayyana cewa kasar ta China na tursasawa Musulmai zuwa wajan wani horo na musamman inda ake azabtar dasu. Saidai kasar ta kare hakan da cewa tana horas da musulman ne ...