
Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta sanar da fara Zabar sabbin ma’aikatan N-Power na Batch C, Duba yanda Zaku ci gaba nema, da Rubuta jarabawa
Gwamnatin tarayya ta sanar da fara zabar Sabbin ma'aikatan N-Power na Batch C inda tace zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 ne ya sa aka sami tsaiko.
Ministar kula da Ibtila'i da Jinkai, Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana haka a ganawa da manema labarai.
Tace an yi tsari wanda yanzu haka an samar da wani shafi na musamman da a nan ne duk wanda ya nemi aikin na N-Power zai shiga ya idasa cike bayanan sa. Tace za'a aikawa duk wanda ya nemi aiki da bayanan yanda zai shiga sabon shafin.
Shafin da za'a shiga din shine, http://www.nasims.gov.ng/
Tace an yi kokari wajan ganin an zabi wanda suka cancanta sannan kuma an baiwa masu larura ra musamman kulawa ta musamman sannan kuma tace bayan mutum ya kammala cike bayanan nasa, zai ci gaba ya rubuta jara...