
NAFDAC ta gargadi yan kasuwa akan amfani da Sinadarai da ke da hatsari ga lafiyar Jama’a domin adana kayan abinci
Hukumar (NAFDAC) ta sake gargadin Jama'a cewa yin amfani da magun-gunan feshi, da duk wasu nau'ikan '' sinadarai (DDVP) wajen adana kayan abinci kan iya zama hatsari ga lafiyar mutane wanda hakan ka iya jawo asarar rai.
Darakta-Janar na hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce, duk gargadin da hukumar tai, amma an samu wasu 'yan kasuwa na cigaba da bijirewa gargadin hukumar wajan cigaba da amfani da sinadaran da aka hana amfani da shi don adana kayan abinci, wanda hakan ke jefa rayuwar masu saye cikin hatsari.
Farfesa Adeyeye ta sake nanata illolin da ke tattare da ci gaba da amfani da Sinadaran, da yawancin jama'a ke amfani dashi, musamman 'yan kasuwar hatsi, da su ka hada da wake da kuma masu saida busassun kifi.
A cewarta, ci gaba da amfani da wadannan magungunan masu h...