Monday, March 30
Shadow

Tag: nafisa abdullahi

Nafisa Abdullahi ta bayyana karin farko da ta hadu da Ali Nuhu

Nafisa Abdullahi ta bayyana karin farko da ta hadu da Ali Nuhu

Nishaɗi
Tauraruwar fina-finan Hausa,Nafisa Abdullahi a sakon data aikewa Ali Nuhu na murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta bayyana yanda suka hadu.   A cikin sakon data saka a shafukanta na sada zumunta,Nafisa ta bayyana cewa, sun hadu karin farko ita da Ali Nuhu a wajan hada fim din (Haaja), ta kara da cewa a karin farko da ya ganta, bata san abinda ya gani ba, yace zai shirya mata fim.   Nafisa ta Kara da cewa daga nanne Ali ya shirya mata shirin fim din Sai Wata Rana kuma duk da yake cewa ita sabuwar Jarumace, ya biyata kudi masu yawa.   A karshe dai Nafisa ta taya Ali Nuhu murnar zagayowar Ranar Haihuwarsa.   https://www.instagram.com/p/B9v8AjenJhE/?igshid=6zavc0sk7tnf
Ji martanin da Nafisa Abdullahi ta baiwa wani da ya ce mata ina bidiyon tsiraicin da tace zata yi?

Ji martanin da Nafisa Abdullahi ta baiwa wani da ya ce mata ina bidiyon tsiraicin da tace zata yi?

Nishaɗi
A kwanakin bayane lokacin dambarwar bidiyon tsiraicin tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth, Abokiyar aikinta, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa itama fa idan ta bushi iska za'a iya ganin hotunanta daga ita sai rigar mama da dan kamfai.   Waccan magana da ta yi ta dauki hankula sosai inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.   Bayan saka Hotunanta a shafinta na Instagram, wani ya cewa Nafisar shin ina maganar bidiyon tsiraicin da tace zata yi?   Sai ta bashi amsar cewa da kwadayinsa zai mutu.  

Kalli kyawawan hotunan Nafisa Abdullahi: Tana kan hanyar dawowa Gida Najeriya daga Ingila

Uncategorized
Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar, ga dukkan alamu Nafisar dai na kan hanyar dawowa gida Najeriya daga kasar Ingila inda taje amso kyautar karramawa da aka mata tare da abokin aikinta Ramadan Booth. Bayan da Ali Nuhu ya musu jagoranci zuwa gurin amsar kyautukan da aka basu, jaruman sunje filin wasan kwallon kafa na kungiyar Chelsea watau Stamford Bridge inda suka kalli wasa tsakanin Chelsea da Manchester United kuru-kuru ba a kwalba ba, irin hotunan na suka wallafa a dandalinsu na shafukan sada zumunta da muhawara sun nuna yanda sukaji dadin hakan Daga nanne kuma da alama kowa ya kama gabanshi, domin ba'a sake ganin jaruman tare ba, ita Nafisa taje ziyara gurin sannanniyar gadar nan ta birnin Landan, sannan kuma ta shiga wani s...