
Gwamnatin tarayya tayi Allah wadai da lalata ofishin jakadancin Najeriya da wasu matasa sukai a kasar Indonesia
'Yan Najeriya mazauna kasar Indonesia sun nuna rashin amincewarsu da batun nuna banbanci da take hakkinsu da jami'an kula da shige da fice dake kasar Indonesiya suke yi musu, inda 'yan Najeriyan suka mamaye ofishin jakadancin kasar Najeriya dake kasar Indonesia tare da lalata wasu kadarorin mallakar gwamnatin Najeriya.
A wani faifan bidiyo da SharaRepoters ya samu, an ga wasu mutane da aka yi imanin cewa 'yan Najeriya ne da ke ɗauke da wasu kwalaye, inda aka ji su, suna kukan cewa “Najeriya bata taimaka mana a kasar nan. Ba mu da wani Ofishin Jakadanci a kasar nan. Ba mu yadda ba.
Idan zaku Iya tunawa cewa wani dan Najeriya dan shekara 41 ya fado daga wani bene hawa na tara a yayin da yake kokarin tserewa daga jami'an shige da fice na kasar Indonesiya bayan da suka kutsa cikin ginin ...