fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Tag: Najeriya Kamaru

Jami’an tsaron Kamaru sun kame wasu mutane 3  ‘yan Najeriya dake garkuwa da mutane

Jami’an tsaron Kamaru sun kame wasu mutane 3 ‘yan Najeriya dake garkuwa da mutane

Tsaro, Uncategorized
Alhaji Idi Amin, Shugaban karamar hukumar Maiha ta jihar Adamawa, ya bayyana cewa Dakarun Tsaron Kamaru sun kama wadanda ake zargi da satar mutane kuma suka tsere zuwa makafarsu dake kasar Kamaru. Shugaban ya tabbatar wa kamfanin dillacin labarai na NAN a ranar Alhamis a hedkwatar karamar Hukumar Maiha. A cewar sa "Wadanda aka kama sun kware wajan garkuwa da mutane da satar dabbobi inda suke da mafaka a kasar Kamaru. Ya bayyana cewa sun tafi zuwa Belel dake buda da Maiha tare da jami'an tsaro don karbo wadan da ake zargi domin mika su ga Jami'an tsaron Najeriya dake Yola.