fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Namibia

Kasar Namibia tace babu ma’aikacin gwamnatin da zai kara sayen sabuwar mota har sai nan da shekaru 5

Kasar Namibia tace babu ma’aikacin gwamnatin da zai kara sayen sabuwar mota har sai nan da shekaru 5

Siyasa
Kasar Namibia dake Kudancin Africa me yawan Al'umma Miliyan 2.5 ta bayyana cewa dalilin matsalar da annobar Coronavirus ta jawowa tattalin arzikinta ta dakatar da sayen sabbin motoci ga ma'aikatan Gwamnati har nan da shekarar 2025.   Kasar tace wannan mataki zai bata damar samun rarar kudi har Dala Miliyan 10.7 wanda tace zata yi amfani dasu wajan ayyuka mafiya muhimmaci a kasar.   Shugaban kasar, Hage G.Geingob ne ya bayyana wannan sanarwar ta shafinsa na Twitter inda kara da cewa hakanan za'a rage yawan amfani da man fetur din da ma'aikatan gwamnati ke yi.   Mutane 16 ne dai suka kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 a kasar amma babu wanda ta kashe.