fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Napoli

Coppa Italia: Inter Milan suna gunadar da atisayi domin daukar fansa anjima tsakanin su da Napoli

Coppa Italia: Inter Milan suna gunadar da atisayi domin daukar fansa anjima tsakanin su da Napoli

Wasanni
Inter Milan sun cigaba da gudanar da atisayi gami da wasan na biyu na Semi final da zasu buga anjima da karfe takwas tsakanin su da Napoli, yayin da yan wasan Antonio Conte suke harin rama kwallon da Napoli suka ci su a wasan farko. A cigaba da buga wasannin kasar Italia bayan cutar korona tasa an dakatar da wasannin har na tsawon watannin hudu. Inter sun shirya rama kwallon da Fabian Ruiz ya ci su a wasan farko yayin da zasu buga wasan ba tare da yan kallo ba. Yan wasan Antonio Conte zasu yi tafiya izuwa Naples domin su kara da Napoli a wasan na biyu na Semi final, yayin da Juventus suka cancanci buga wasan karshe na gasar Coppa Italia a daren jiya saboda kwallon da suka ci wadda ba ta gida ba.