fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: NAPTIP

Shugaba Buhari yayi sabon nadi a hukumar NAPTIP

Shugaba Buhari yayi sabon nadi a hukumar NAPTIP

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Imaan Sulaiman-Ibrahim a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP).   Wannan na kunshe ne a cikin wani takaitaccen bayani ga jaridar DAILY POST a ranar Talata dauke da sa hannun Garba Shehu, kakakin shugaban kasar. Mrs Sulaiman-Ibrahim, wata mai rike da digirin BSc (Sociology), Masters of Arts (Management) da kuma Masters of Business Administration (MBA), wadda yar asalin jihar Nasarawa ce.   Kafin sabon nadin nata, ta kasance mamba a Majalisar Shawara kan Tattalin Arziki ta Jihar Nasarawa sannan kuma mai ba da shawara na musamman kan dabarun sadarwa ga Karamar Ministar Ilimi.