fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: NCC

Hukumar NCC ta bada umarnin dakatar da saida sabbin SIM da yin rajista

Hukumar NCC ta bada umarnin dakatar da saida sabbin SIM da yin rajista

Uncategorized
Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta umarci masu kamfonan hanyar sadarwa ta Wayar Hannu da su hanzarta dakatar da sayar da sabbin katinan SIM don ba da damar tantance bayanan mutanen da suka yi rajista. Daraktan hulda da jama’a na NCC, Dr. Ikechukwu Adinde, a wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce ya zama dole ga masu aiki su bi har sai an kammala aikin tantancewar. A cewarsa, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Dr Isa Pantami, ya umarci hukumar da ta fara binciken kwastomomin masu rajista. Amma, ya ce za a iya bayar da izinin sayan bayan amincewa daga Gwamnatin Tarayya ta hannun hukumar. Ya yi gargadin cewa rashin bin umarnin hakan zai gamu da tsauraran hukunci, gami da yiwuwar janye lasisin aiki. Adinde ya ce binciken zai taimaka wajen karfafa nasarar aikin rajis...
Buhari Ya Turawa Majalisar Dattawa Sunan Danbatta Don Tabbatar dashi a matsayin shugaban Hukumar NCC

Buhari Ya Turawa Majalisar Dattawa Sunan Danbatta Don Tabbatar dashi a matsayin shugaban Hukumar NCC

Siyasa
Majalisar dattijan Najeriya a ranar Talata ta sanar da wata tattaunawa ta zartarwa daga Shugaba Muhammadu Buhari da ke neman amincewa da Farfesa, Umar Danbatta a matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya na wa’adi na biyu. A wata wasika da aka karanta a gaban majalisar dattijai ta hannun Shugaban, Dakta Ahmad Ibrahim Lawan, tabbatarwar ta yi daidai da tanadin sashi na 8, sakin layi na 1 na Dokar Sadarwa ta Najeriya (NCC) 2003. Wani sashi na wasikar ya ce: "ina farin cikin gabatarwa da Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Farfesa Umar Danbatta a matsayin Mataimakin Shugaban kwamitin riko na Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya (NCC) a karo na biyu na shekaru biyar. "Ina fata Majalisar Dattawa za ta duba kuma ta tabbatar da wadanda aka zaba kamar yadda ...
Yanzu-Yanzu:Shugaba Buhari ya sake nada Umar Danbatta matsayin shugaban hukumar sadarwa ta NCC

Yanzu-Yanzu:Shugaba Buhari ya sake nada Umar Danbatta matsayin shugaban hukumar sadarwa ta NCC

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Umar Danbatta a matsayin hmshugaban hukumar Sadarwa da NCC a karo na 2.   Shugaba Buhari ne dama ya nada Danbatta wanda Farfesa ne a fannin Kimiyyar Sadarwa shekaru 4 da suka gabata a kan mukamin. Me magana da yawun ma'aikatar Sadarwa da tattalin arzikin zamani,Uwa Sulaiman ce ta bayyana haka a sanarwar data fitar me sa hannun ministan ma'aikatar, Dr. Isa Ali Pantami.   Pantami ne ya bayar da shawarar sake nada Danbatta akan wannan mukami wanda kuma shugaba Buhari ya amince da wannan shawara.