
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta bayyana rashin jin dadinta kan halin da jihar kano ta tsinci kanta a ciki
Shugaban hukumar NCDC Dr Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana haka, yayin da yake ganawa da kwamitin karta kwana na gwamnatin tarayya dake ganawa a Abuja, inda ya ce hukumar ta damu matuka kan halin da jihar ta tsinci kanta.
A cewar sa "Mun rufe wurin gwajin ne, amma kuma zamu bude shi, amma kuma nan bada jimawa ba wasu guraran gwajin guda biyu zasu fara aiki dan cigaba da gwajin cutar, sannan muna cigaba da aiki da gwamnatin kano wajan cigaba da yaki da cutar.
Gwamnan kano ya dai yi kukan cewa hukumar NCDC bata ce komai ba kan jihar sakamakon halin da jihar ta tsinci kanta a ciki ba.