fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Tag: NDDC

Shugaba Buhari zai kaddamar da Ginin Biliyan 16 na hukumar raya yankin Naija Delta, NDDC

Shugaba Buhari zai kaddamar da Ginin Biliyan 16 na hukumar raya yankin Naija Delta, NDDC

Siyasa
A ranar Alhamis me zuwa ne ake sa ran shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kaddsmar da ginin hukumar raya yankin Najeriya Delta ta NDDC da aka yi akan Naira Biliyan 16.   An fara ginin hukumar ne tun shekarar 1996. Ministan kula da harkokin Naija Delta, Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin da yake ganawa da mane Labarai a Fatakwal, Jihar Rivers.   Yace tun da aka fara ginin a shekarar 1996 ya rika tafiyar Hawai iya sai zuwa gwanatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne aka kammalashi.   “The road to completion of the over N16 billion NDDC office edifice started when I visited the building in 2019 and learnt that the project commenced 25 years ago in 1996. “After the visit, I briefed President Buhari and told him that we can make the buil...
Ku gaya mana wanda suka saci kudin mu babu wata tarwatsewa da Najeriya zata yi>>Dan Jarida ya gayawa NDDC

Ku gaya mana wanda suka saci kudin mu babu wata tarwatsewa da Najeriya zata yi>>Dan Jarida ya gayawa NDDC

Siyasa
Wani dan Jarida, Mr. Iteveh Ekpokpobe ya jawo hankalin hukumar NDDC da cewa ta fito ta bayyanawa Najeriya wanda suka saci kudin hukumar hakan ba zai sa Najeriya ta tarwatse ba kamar yanda suka yi ikirari.   Yace bayyana wanda suka saci kudin zai taimaka wakajan yaki da rashawa da cin hanci da gwamnati takr. Hutudole ya samo muku cewa dan jaridar ya koka da cewa rashawa da cin hancine suka hana yankin na Naija Delta ci gana.   A baya mun ji daraktan bada kwangila na ma'aikatar ta Naija Delta, Cairo Ojougboh yana cewa idan ya fallasa masu sadar kudi a ma'aikatar ta NDDC Najeriya zata tarwatse.
Idan Muka Fallasa wanda suka saci kudi, Najeriya zata tarwarse>>NDDC

Idan Muka Fallasa wanda suka saci kudi, Najeriya zata tarwarse>>NDDC

Siyasa
Hukumar wucin gadi dake kula da gudanar da hukumar raya yankin Naija Delta ta bayyana cewa idan fa ta fallasa wanda suka ci kudi a ma'aikatar to Najeriya zata tarwatse.   Daraktan dake kula da bada kwangila na ma'aikatar Dr. Cairo Ojougboh ya bayyana haka ga manema labarai na Vanguard.  Hutudole ya fahimci cewa yace akwai manyan mutane dake ci da maaikatar wanda idan hukumar ta fallasa su akwai matsala. Hakanan ya zargi majalisar tarayya da da yiwa aikin binciken da shugaban kasa yasa a yi na ayyukan NDDC zagon kasa. Yace 'yan Majalisar na binciken dodorido ne kawai sannan kuma suka ki amincewa sa kasafin kudin hukumar wanda hakan zai kawo cikas ga aikin binciken da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sa a yi.   Yace 'yan Najeriya su jira su gani bayan Binciken ...
EFCC ta fara Bincikar Ministan Naija Delta>>Godswill Akpabio

EFCC ta fara Bincikar Ministan Naija Delta>>Godswill Akpabio

Siyasa
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukukar hana cin hanci ta EFCC tuni ta fara bincikar Ministan Naija Delta, Godswill Akpabio da kuma shugaban hukumar raya yankin ta NDDC, Farfesa Kemebradikumo Pondei kan zargin Almundahanar Kudi.   Hakan ya tabbatane a wasikar da EFCC ta aikewa da wata kungiya me rajin dabbaka kyakyawan Jagoranci da kuma 'yanci karkashin shugabancin Deji Adeyanju. Kungiyar ta aikewa da EFCC bukatar bincikar Akpabio akan zargin lakume Biliyan 40 kuma tuni EFCC tace ta fara wannan binciken.  
Suman da na yi da gaske ne fa amma abin ya bani mamaki da naji ‘yan Najeriya na cewa wai na karyane>>Pondei

Suman da na yi da gaske ne fa amma abin ya bani mamaki da naji ‘yan Najeriya na cewa wai na karyane>>Pondei

Siyasa
Shugaban hukumar raya yankin Naija Delta, farfesa Kemebradikumo Pondei ya bayyana mamakinsa da saboda yanda 'yan Najeriya suka rika cewa wai sumar da yayi a gaban 'yan Majalisa ta karyace.   Pondei ya suma a gaban kwamitin hadakar majalisun wajilai dana Dattijai a yayin da ake tuhumarsa kan batan Biliyoyin Naija a ma'aikatar. Hutudole ya ruwaito muku Yanda Lamarin ya kasance inda daga karshe saidsi fita aka yi dashi daga majalisar. Amma a hirr da yayi da Vanguard bayan ya warke, ya bayyana cewa yayi mamaki da yaji 'yan Najeriya na cewa suman karya yayi.   Yace abune ya sameshi wanda shi kanshi bai yi tsammani ba kuma bai san da me zai kirashi ba. Ya kuma kara da cewa baya fatan hakan ta faru da wani.
Duk da umarnin shugaba Buhari, NDDC har yanzu bata biya kudin karatun dalibai data aika karatu kasar waje ba

Duk da umarnin shugaba Buhari, NDDC har yanzu bata biya kudin karatun dalibai data aika karatu kasar waje ba

Uncategorized
Bayan da daliban da hukumar kula da yankin Naija Delta, NDDC ta tura karatu kasar waje su ka yi zanga-zanga na rashin biyansu kudin makaranta, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci da Hukumar ta biya kudin makarantar.   Saidai bincike ya bayyana cewa kwanaki 10 kenan bayan umarnin na shugaban kasa, Muhammadu Buhari amma har yanzu NDDC bata biya kudin karatun dalibanba. Hutudole ya fahimci cewa an baiwa kowane dalibi Dubu Dari 5 sannan kuma daga baya zaa baiwa kowanne dala Dubu 30 a matsayin kudin Makaranta. Saidai binciken Punch ya bayyana cewa tun bayan da aka baiwa Daliban Naira Dubu dari 5, har yanzu ba'a basu sauran kudin ba, wanda hakan yasa suke fuskantar barazanar kora daga makarantun da suke karatu a kasashen waje. Dalilin hakane yasa suka yi zanga-zanga. &...
NDDC ta aikewa shugaban ‘yansanda Bukatar ya binciki wasu manyan jami’ansa da suka baiwa Makudan kudaden Kwangila amma basu yi aikin ba

NDDC ta aikewa shugaban ‘yansanda Bukatar ya binciki wasu manyan jami’ansa da suka baiwa Makudan kudaden Kwangila amma basu yi aikin ba

Siyasa
Hukumar kula da yankin Naija Delta, NDDC ta aikewa shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris cewa ya binciki wasu manyan 'yansanda da hukumar ta baiwa aikin kwagila na Miliyoyin Naira suka cinye kudin ba tare da an gudanar da aikin ba.   Daraktan hukumar Kemebradikumo Pondei ne ya aikewa shugaban 'yansandan da wannan bukata. Ya kara da cewa rashin gudanar da aikin ya shafi rayuwar mutanen yankin sosai dan haka a yi bincike.
An kaiwa majalisa sabon zargin Almundahanar Biliyoyin Naira akan Shugaban NDDC da ya suma a gabanta

An kaiwa majalisa sabon zargin Almundahanar Biliyoyin Naira akan Shugaban NDDC da ya suma a gabanta

Siyasa
Rahotanni daga Abuja na cewa an kaiwa Majalisar Dattijai sabon zargin wasu Biliyoyin Naira akan shugaban hukumar kula da yankin Naija Delta,  Kemebradikumo Pondei banda wanda yanzu haka take bincikensa akai.   Majalisar ta kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba za'a fara binciken Pondei akan wannan sabbin zarge-zargen dan zai sake gurfana a gabanta. A yanzu dai haka majalisa na binciken badakalar Biliyan 40 a ma'aikatar ta NDDC wadda lokacin bincikenne, Pondei ya suma.   Saidai sanata me kula da kwamitin Binciken,Sanata Ayo Akinyelure ya bayyanawa Majiyarmu ta Punch cewa zasu gayyaci shugaban na NDDC ya musu bayanin zargin da kuma sanatocin da hukumar ke ikirarin baiwa ayyukan kwangila.
A karshe dai Akpabio ya bayyana ‘yan Majalisar dake amfana da Kwangilar NDDC

A karshe dai Akpabio ya bayyana ‘yan Majalisar dake amfana da Kwangilar NDDC

Siyasa
Ministan harkokin Naija Delta, Godswill Akpabio ya bayyana 'yan Majalisar wakilai dake amfana da kwangilolin ma'aikatar NDDC kamar yanda majalisar ta bukata.   Saidai be bayyana cewa ko sun amfana da kwangilar bane a kai tsaye ko kuma sun baiwa wasu na kusa dasu bane. Daga cikinsu akwai Nicholas Mutu me wakiltar Bamadi/Patani daga jihar Delta wanda yace ya samu kwangiloli 74.   A baya dai EFCC ta tuhumi wannan dan majalisa da aikata ba daidai ba da Miliyan 320.   Akwai shugaban kwamitin majalisar kan NDDC, Peter Nwaoboshi da ya amfana da kwangiloli 53. Sai Matthew Urhoghide da ya amfana da kwangiloli 6 sai James Manager da shima ya amfana da kwangiloli 6, da Samuel Anyanwu da ya amfana da kwangiloli 19, sai kuma sauran da yace sun fito daga jihohin O...
Babu wata gadar da muka gida akan Biliyan 2.3>>NDDC ta karyata hoton gadar katako dake yawo a shafukan sada zumunta

Babu wata gadar da muka gida akan Biliyan 2.3>>NDDC ta karyata hoton gadar katako dake yawo a shafukan sada zumunta

Siyasa
Hukumar kula da ci gaban yankin Naija Delta, NDDC ta karyata hoton gadar Katako dake yawo a shafukan sada zumunta da ake cewa ta gina akan Naira Biliyan 2.3.   Hukumar tace wannan labarin ba gaskiya bane. Gadar dake Elebele, Jihar Bayelsa ta rika yawo a shafukan sada zumunta inda akace NDDC ce ta ginata akan Biliyan 2.3. Saidai a ta bakin daya daga cikin daraktocin NDDC, Charles Obi Odili ya bayyana cewa mutanen yankin sun samesu inda suka bukaci da a gyara musu gadar su da ta rushe. Yace basu kai ga yin aikin ba tukuna.   Yace mutanen yankinne suka yi aikin gayya suka yi wannan gadar katako da ake gani amma ba NDDC ba.   Yayi zargin cewa, wasu ne dake son baya sunan ma'aikatar suka dauki nauyin wannan aiki. Inda yace kada mutanen yankin su biye musu...