
Shugaba Buhari bai damu da ci gaba da tsaron Arewaba>>Kungiyar Dattawan Arewa
Kungiyar dattawan Arewa ta NEF ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai damu da ci gaba da tatalin arziki da kuma tsaro a Arewa ba.
Kakakin kungiyar, Dr. Hakeem Baba Ahmad ne ya bayyana haka a sanarwar da kungiyar ta fitar inda yace labarin aikin titin Abuja zuwa Kano bai zo musu da dadi ba.
Yace wannan titi an bayar da aikinsa a shekarar 2017 amma bai fara aiki ba sai shekarar 2018 wanda kuma yake tafiyar hawainiya kuma an ce nan da shskaru 5 ma ba zai kammaluba. Yace wannan titi shine kusannan babar hanyar data hada Arewa da Kudu kuma lalacewarsa yasa ya zama inda masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka.
Yace tun a zaben shekarar 2019, saida wannan kungiya tasu ta gargadi 'yan Arewa cewa kada su zabi shugaban kasa, Muhammadu Bu...