fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Neja

Gwamnatin Neja ta ceto matafiya 10 daga cikin 21 da ‘yan bindiga suka sace

Gwamnatin Neja ta ceto matafiya 10 daga cikin 21 da ‘yan bindiga suka sace

Crime
Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da ceto akalla mutane 10 daga cikin mutane 21 da 'yan bindiga suka sace a jihar. Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Mohammad Dani Idris, shine ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Talata, a Babban Asibitin jihar dake Minna a a yayin da likitoci ke duba lafiyar wadanda aka ceto. Hakanan kwamishinan ya musanta rade-radin biyan fansa wajan ceto wadanda a kai garkuwa dasu inda ya shaida cewa gwamnati tabi wasu dabaru ne wajan ceto mutanan.
Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello ya sha Al’washin kara kaimi wajan tabbatar da tsaro a jiharsa

Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello ya sha Al’washin kara kaimi wajan tabbatar da tsaro a jiharsa

Kiwon Lafiya
Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yi Allah wadai da kakkausar murya game da sace fasinjoji 20 a kauyen Kundu da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja. Gwamna Sani Bello a cikin wata sanarwa ya bayyana lamarin a matsayin halin rashin kirki, inda ya kara da cewa gwamnati za ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi. Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ba za ta mika wuya ga masu aikata miyagun laifuffuka a jihar ba da suka hada da 'yan fashi, masu satar mutane da barayin shanu, A cewarsa Gwamnatinsa zata ci gaba da amfani da wadatattun kayan aiki da ma'aikata don dakile matsalar.
Wani shugaban karamar Hukuma a jihar Neja ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Wani shugaban karamar Hukuma a jihar Neja ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Siyasa
Shugaban karamar hukumar Magama a jihar Neja Alhaji Safyanu Yahaya dake Jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Sauya shekar shugaban na zuwa ne mako daya kacal bayan da jam’iyyar ta fadi babban zabe na majalisar wakilai  wanda jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta lashe. Sanarwar ta fito ne ta hannun Shugaban jam'iyyar APC dake mazabar Magama a jihar Neja.  
APGA ta lashe zaben cike gurbi a jihar Neja

APGA ta lashe zaben cike gurbi a jihar Neja

Siyasa
Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata A Mazabar Magama / Rijau dake jihar Neja. Dan takarar jam'iyyar APGA, Salihu Salleh shine wanda ya samu Nasara da yawan kuri’u 22,965 yayin da Dan takarar Jam'iyyar PDP  Emmanei Alamu Endoz ya samu kuri'u 22,507 da aka jefa. Dan takarar Jam'iyyar ADC, Halilu Yussuf Al ya samu kuri’u 316; sai dai babu Jam'iyyar APC a zaben da aka gudanar.  
Gwamnatin Jihar Neja ta umarci makarantu da su koma bakin aiki a ranar 25 ga watan Janairu

Gwamnatin Jihar Neja ta umarci makarantu da su koma bakin aiki a ranar 25 ga watan Janairu

Uncategorized
Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta gyara Manhajar zangon karatu na shekarar 2020/2021 inda wa'adin farko, zai fara daga ranar Litinin, 4 ga Janairu, 2021,Wanda a yanzu sabuwar ranar zata kasance ranar Litinin, 25 ga watan Janairun 2021, tana mai cewa sabuwar ranar ita ce ranar da za a dawo da ayyukan ilimi a duk makarantun firamare da sakandare a jihar. Kwamishina, Ma’aikatar Ilimi, Hajiya Hannatu Jibrin Salihu ce ta bayyana hakan a karshen mako yayin da take tattaunawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar. Hakanan kwamishinan ta bukaci Makarantu dasu bi ka'idojin cutar Covid-19 wajan sanya ta kunkumin rufe hanci, wanke hannaye, da kuma bada tazara.
Gwamna Bello na  jihar Neja ya yi Allah wadai da hare-haren ‘yan bindiga Dake addabar al’ummomi jihar

Gwamna Bello na jihar Neja ya yi Allah wadai da hare-haren ‘yan bindiga Dake addabar al’ummomi jihar

Tsaro
Wasu 'Yan bindiga a jihar Neja sun sace mutane a kalla 20 a yayin da suka kai wani hari kan wasu al'ummomi a jihar. A sakon da Gwamnan jihar ya aike yayi Allah wadai da harin da 'yan bindigar suka kai na baya-bayannan a kauyukan Maitumbi da Kuchi dake kananan hukumomin Bosso da munya na jihar. Sanarwar wacce babban sakataran gwamnan ya fitar a ranar Litinin Misis Mary Noel-Berje yayi Allah wadai da harin inda kuma ya roki jama'a da su marawa gwamnatin jihar na kokarin da take wajan samar da tsaro da kuma fatattakar 'yan bindiga a jihar.
Hadarin Mota ya lakume rayukan mutum 6 tare da jikkata wasu a jihar Neja

Hadarin Mota ya lakume rayukan mutum 6 tare da jikkata wasu a jihar Neja

Uncategorized
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC) na Jihar Neja, Mista Joel Dagwa, ya tabbatar da mutuwar mutane shida a wani hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Bida-Kutigi na jihar a ranar Alhamis. Mista Dagwa ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Tribune  a ranar Juma'a a Minna babban birnin jihar, a wata hira ta wayar tarho, inda ya tabbatar da mutuwar wasu mutum 6 tare da jikkatar wasu mutum hudu wadanda suka samu raunuka daban-daban. A cewarsa, hatsarin ya faru ne da misalin karfe 6:20 na safiya a kauyen Jifan da ke kan titin Bida-Mokwa a karamar hukumar Bida ta jihar wanda ya rutsa da wata motar  bas mai daukar mutane 18 mai lamba JJJ 132 XV. Shugaban FRSC din ya kara da cewa motar ta tashi daga Bida, inda ta nufi Kutigi lokacin da hatsarin ya faru. Hakanan kwamandan ya dang...
Gwamnatin Jihar Neja ta roki Kungiyar ‘yan Kwadago data janye yajin aiki

Gwamnatin Jihar Neja ta roki Kungiyar ‘yan Kwadago data janye yajin aiki

Uncategorized
Gwamnatin jihar Neja ta aike da kira zuwa ga kungiyar 'yan kwadago ta Najeriya (NLC) da ta rungumi tattaunawa da fahimtar juna ta hanyar janye yajin aikin da kungiyar ta shiga  don ci gaban jihar baki daya. Kwamishinan Kudi, Alhaji Zakari Abubakar shine ya yi wannan rokon a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Minna. A cewarsa, Gwamantin jihar, A shirye take ta ci gaba da tattaunawa kan bambance-bambancen da ke tsakaninta da kungiyar 'yan kwadagon. Hakanan yayi kira da cewa, ya kamata kungiyar ta sassauta tare da yin duba kan batun yajin aikin domin jihar ta cigaba. Ya ci gaba da bayanin cewa jinkirin biyan albashin ma'aikatan jihar ba da gangan ba ne, yana mai cewa, gwamnati mai ci a yanzu karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello tana da kishin far...
Gwamanan Neja ya yi al’kawarin daukar Nauyin karatun Iyalan ‘yan kungiyar sa kai da ‘yan bindiga suka kashe a jihar

Gwamanan Neja ya yi al’kawarin daukar Nauyin karatun Iyalan ‘yan kungiyar sa kai da ‘yan bindiga suka kashe a jihar

Tsaro
Gwamna Bello ya yi alkawarin daukar nauyin karatun yaran 'yan banga da' yan bindiga suka kashe Gwamn Sani Bello na jihar Neja a ranar Asabar ya yi alkawarin daukar nauyin karatun 'ya 'ya ga mambobin kungiyar 'Vigilance Group of Nigeria (VGN)' wadanda suka rasa rayukansu a yaki da 'yan fashi. Bello ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da jami'ai da mambobin kungiyar sa kai a garin Kontagora, a jihar Neja. Haka zalika Gwamanan Ya yaba wa kokarin  'yan kungiyar sakan, wajan nuna jarumta ta hanyar kai hari maboyar' yan ta'addan, inda ya bayyana cewa ya zama wajubi a ya ba musu. Hakanan Gwamnan ya bayar da umarnin a tattara bayanan wadanda 'yan fashin suka kashe, inda ya bukaci da a mika su izuwa  Ma'aikatar Kananan Hukumomin jihar. Baya ga haka, Gwamanan ya kuma bada g...
‘Yan Sanda A jihar Neja sun cafke wasu Mutane 3 da ake zargi da laifin satar man fetur

‘Yan Sanda A jihar Neja sun cafke wasu Mutane 3 da ake zargi da laifin satar man fetur

Crime
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da dibar man fetur daga bututun da aka lalata a kauyen Numba-Gwari da ke karamar hukumar Suleja ta jihar. Bututun wanda mallakar kamfanin man fetur na kasa ne (NNPC). Jami'in hulda da jama'a na rundunar (PPRO), ASP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a a  wata sanarwa da ya fitar a Minna. Abiodun ya bayyana hakan da cewa, a ranar 13 ga watan Nuwamba da misalin karfe 09:00, rundunar 'yan sandan jihar ta yi nasarar cafke wadanda ake zargin biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu. Haka zalika rundunar ta bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka Daniel Joshua, Mai shekaru 37, sai  Sunday Ezekiel, Mai shekara 33 da Suleiman Madaki, Mai shekaru 29, dukkaninsu mazauna kauyen Numba-Gwari da ke ...