fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Tag: Nelson Mandela

Diyar Tsohon Shugaban Kasar Africa Ta Kudu, Nelson Mandela Ta Mutu

Diyar Tsohon Shugaban Kasar Africa Ta Kudu, Nelson Mandela Ta Mutu

Siyasa
Zindzi Mandela, karamar ‘yar Nelson Mandela, bakin mutum na farko da ya mulki kasar Afirka ta Kudu ta mutu tana da shekara 59 a duniya. Ta mutu ne da safiyar ranar Litinin a wani asibiti dake birnin Johannesburg, a cewar gidan talabijin din kasar na SABC. Kafin rasuwarta, ita ce jakadar Afirka ta Kudu a kasar Denmark. Sai dai, har yanzu ba a bayyana yadda ta mutu ba. Zindzi Mandela ita ce ta shida a cikin jerin ‘Yayan Mandela, amma kuma ta biyu a wajen mahaifiyarta Winnie Madikizela-Mandela, matarsa ta biyu. Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, cikin wani sanarwar ta’aziyya ya ce “Zindzi Mandela ta taka gagarumar rawa wajen fafutukar kakkabe wariya don launin fata a kasar. Bata taba kasa gwiwa ba, wajen kwato mana ‘yancinmu”. An ...