fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: NEMA

Hukumar bada agajin gaggawa NEMA Ta Raba Kayan Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ta Shafa A Enugu

Hukumar bada agajin gaggawa NEMA Ta Raba Kayan Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ta Shafa A Enugu

Uncategorized
A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta raba kayayyakin tallafi na miliyoyin nairori ga al’ummomin da ambaliyar ta shafa a shekarar 2020 dake karamar hukumar Uzo Uwani ta Jihar Enugu. Kayayyakin agajin, wadanda suka hada da kayan abinci da sauransu. Hukumar ta  rarraba kayan ne zuwa garuruwa uku da suka hada da Ojor, Ogurugu da Igga. Da yake magana a garin Ojor, Kodinetan NEMA na yankin, Mista Fred Anusim, ya ce ambaliyar ta lalata gonaki da gine-gine da dama a yankunan tun a ranar 3 ga watan Oktoban shekarar bara data wuce 2020.
Hukumar NEMA Ta Musanta Korar Ma’aikata 48

Hukumar NEMA Ta Musanta Korar Ma’aikata 48

Siyasa
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa ta musanta korar ma’aikata 48. An ruwaito a baya cewa NEMA ta dauki ma’aikata 48, amma ta sallame su bayan shekara guda da fara aikin. Jami'in hulda da jama'a na NEMA, Manzo Ezekiel, a wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya ce duk da cewa an dauke su aiki, amma ba a kore su ba. Ya ce NEMA ta “soke” daukar ma’aikatan don rashin bin “ka’idojin da aka gindaya don daukar ma’aikatan gwamnati.” Ezekiel ya taba shaidawa Aminiya cewa bai san da daukar ba. Ya ce duk da cewa an samu amincewar daga Hukumar NEMA ta Gwamnati don daukar ma’aikata a shekarar 2018, amma ba a samu amincewar daga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Tarayya da na Ma’aikatar Harkokin Jin Kai ba. "Game da zargin cewa ba a biya albashin wadannan da aka dauka ba na shekara ...
Hukumar bada a gajin gaggwa ta NEMA ta gargadi Direbobi kan tukin ganganci

Hukumar bada a gajin gaggwa ta NEMA ta gargadi Direbobi kan tukin ganganci

Tsaro
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta wayar da kan direbobi tare da gargadin su kan kaucewa tukin ganganci a yayin bukukuwan karshan shekara. Kodinetan hukumar NEMA mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Ado Sanusi shine ya bayyana hakan a yayin da yake wayar da kan Direbobi a jihar Kano kan kaucewa Tukin ganganci, inda ya ce lalle kiran ya zama wajubi sabuda yawan afkuwar hadura da ake samu akan manyan titunan kasar. A cewarsa, akwai bukatar direbobin da ke tafiye-tafiye da su kiyaye tare da takaita gudu a yayin da suke tuki domin kaucewa afkuwar hadura.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa Ta Kasa (NEMA) Ta Raba Kayan Abinci A Sansanonin Yan Gudun Hijira A Jihar Adamawa

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa Ta Kasa (NEMA) Ta Raba Kayan Abinci A Sansanonin Yan Gudun Hijira A Jihar Adamawa

Siyasa
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta rarraba kayayyakin abinci ga yan gudun hijira 3,936  a cikin sassanonin yan gudun hijira na Fofure da George Theresa da Malkohi da ke jihar Adamawa. Mista Iliya Midala, Shugaban Ayyuka a Adamawa da Taraba yayin rabon kayan, ya ba da jaddawalin yadda aka raba kayan Ga Sansanonin da suka hada da Malkohi 1,434, Fufore 1,974 da Theresa 528 duk sun amfana daga rabon kayan. Iliya ya ce abubuwan da aka rarraba sune shinkafa, wake, tumatirin kwankwani, kayan dandano da gishiri. Ya ce karkashin amincewar da Darakta Janar na NEMA, AVM Muhammed Alhaji Muhammed mai ritaya ya bayar. Ana kai ma Yan gudun hijirar a cikin jihar kayan ne na wata-wata. Bakura Umar, Shugaban IDPs ya yaba da karimcin daga gwamnatin tarayya ya kuma yi kira da a ...
Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta Fara Rabon Kayan Agaji a Jihar Kwara

Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta Fara Rabon Kayan Agaji a Jihar Kwara

Siyasa
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta fara raba kayan agaji ga gidaje a mazabar yankin Kwara ta Arewa. Sama da gidaje 662 a kananan hukumomin Kaiama, Baruten da Edu iska da ruwan sama mai karfi ya shafa. NEMA ta rarraba abinci da wasu abubuwan da ba abinci ba ga mutanen da abin ya shafa don yin magance radadin da bala’in da ta same su tare da basu damar sake ci gaba da rayuwarsu. Abubuwan sun hada da buhunan shinkafa 662 (12.5kg), jaka 662 na masara (12.5kg), jaka 662 na wake (25kg), jaka 66 na sukari, 66 na man girki da katifu 1,300. Sauran sun hada da bargo 1,300, 1,300 na ragar sauro, jakar siminti1,200, kayan rufin gida 1,000, jakar kusa inci 3 guda 175, da kuma fakitoci 350 na kusosin, zinc. Rabon kayan na kwana biyu ya fara ne a ranar Asabar a Ilakpa, ...