fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Nigeria Lebanon

‘Yan Mata 27 da suka makale a kasar Lebanon sun dawo gida Najeriya

‘Yan Mata 27 da suka makale a kasar Lebanon sun dawo gida Najeriya

Tsaro
Wani rukuni na wasu 'yan matan Najeriya su 27 tare da sauran 'yan Najeriya mazauna  kasar lebanon sun isa Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ranar Lahadi, bayan da gwamnatin Najeriya ta kwashe su daga kasar. Da yake karbar su, Mista Ferdinand Nwonye, ​​Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje wanda ya wakilci Ministan  Harkokin Wajen, Mista Geoffrey Onyeama, ya ce an kwashe 'yan Najeriyan ne, domin cika alkawarin da gwamnatin tarayyan Najeriya ta yi na tabbatar da cewa ba wani dan Najeriya da za a bari ya kasance  zaune a kasar Lebanon.   Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa 'yan Najeriya da suka makale a kasar sun yi ta rokon Gwamnatin Najeriya da ta kawo musu a gaji su dawo gida.