
Gwamnatin tarayya: Najeriya da wasu kasashan Afurka na shigo da kayayyaki na kimanin Dala billiyan $650 daga kasashan waje
Kwamitin Ayyukan Kasa na Najeriya kan harkokin Kasuwanci, a ranar Litinin ya ce Najeriya da sauran kasashe a Nahiyar Afirka kan kashe dala biliyan 650 a duk shekara ta hanyar shigo da kayayyaki daga sauran kasashen duniya.
Sanarwar hakan na kunshe ne ta cikin jawabin da Sakatare janar na zartarwa AfCFTA NAC, ya bayyana Francis Anatogu
Haka zalika Gwamnatin Tarayya ce ta kafa kwamitin a watan Disamba na shekarar 2019.