fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Nijar

Shugaba Buhari ya karbi lambar yabo mafi girma ta Jamhuriyar Nijar

Shugaba Buhari ya karbi lambar yabo mafi girma ta Jamhuriyar Nijar

Siyasa
Shugaba Mahamadou Issoufou ya ba Shugaba Muhammadu Buhari lambar yabo mafi girma ta Jamhuriyar Nijar, Grand Croix Des Ordre National Du Niger. A ranar Talata, Issoufou ya ce an karrama shi ne saboda "kuzarinsa, kishin kasa da kuma himmar ciyar da Afirka gaba, farawa daga Yammaci". Issoufou ya gode masa da ‘yan Najeriya kan goyon bayan da ya samu a matsayinsa na shugaban kasarsa tsawon shekaru goma, musamman a lokacin Buhari a matsayin Shugaban ECOWAS, inda ya bayyana Najeriya a matsayin“ gida na biyu ”. A cikin jawabin nasa, Buhari ya jinjina wa shugaban mai barin gado saboda kiyaye ka’idojin dimokiradiyya, inganta tattalin arziki da kuma karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu. Ya lura cewa nasarorin da Issoufou ya samu ya samu karbuwa sosai ciki har da la...
Allah ne kadai zai iya kare iyakar Najeriya da Nijar amma ba Mutum ba>>Shugaba Buhari

Allah ne kadai zai iya kare iyakar Najeriya da Nijar amma ba Mutum ba>>Shugaba Buhari

Tsaro
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Allah ne kadai zai iya kare iyakar Najeriya da Nijar yadda ya kamata wadda fadinta ya kai kilometer 1,400.   Ya bayyana hakane a fadarsa yayin da yake ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasa,  Namadi Sambo wanda kuma shine shugaban tawagar ECOWAS kan zabe zuwa Nijar din.   Shugaba Buhari ya ce daga Daura ya fito dan haka yana da masaniya akan kasar Nijar, yace shugaban ta me barin gado mutumin kirki ne kuma suna tuntubar juna akai-akai.   Ya bayyana cewa, akwai iyakar Najeriya da Nijar wadda fadinta ya kai Kilometer 1,400 wadda kuma Allah ne kadai zai iya kare ta yanda ya kamata. Shugaban yace zasu baiwa Nijar dukkan goyon bayan da ya kamata dan ganij an yi zabe cikin Nasara. PRESIDENT BUHARI PLEDGES ...
Buhari ya aika da sakon ta’aziyyar mutuwar tsohon shugaban kasar Nijar, Tandja

Buhari ya aika da sakon ta’aziyyar mutuwar tsohon shugaban kasar Nijar, Tandja

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Mamadou Tandja, tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Nijar. Ya mutu a ranar Talata yana da shekaru 82 bayan shekaru da rashin lafiya. A ranar Laraba, Buhari ya ce Nijar ta yi rashin wani tsohon shugaba wanda ke da kwarewar soja, siyasa da kuma mulki. Shugaban ya yaba da irin gudummawar da marigayin ya bayar a fagen soja da kuma fagen siyasar kasarsa. Shugaban na Najeriya ya yi fatan Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar, dangin Tandja da sauransu karfin gwiwar jure rashin. "Gwamnati da mutanen Najeriya na tare da dukkan mutanen Nijar a wannan lokacin na bakin ciki," sanarwar ta'aziyyar Buhari da kakakin shi, Garba Shehu ya fitar.
Matasa na kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta kammala Titin jirgin kasa zuwa kasar Nijar dan su je auro matan kasar

Matasa na kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta kammala Titin jirgin kasa zuwa kasar Nijar dan su je auro matan kasar

Nishaɗi
Wasu matasa sun fara kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya gaggauta kammala aikin titin jirgin kasa da zai tashi daga Kano zuwa Nijar dan su je su auro kyawawan matan kasar.   Waninkatashine ya fara yin wannan kira ta shafinta na Twitter inda ya saka kyawawan hotunan matan kasar Nijar din. https://twitter.com/Abkr_Maikudi/status/1311005972144496644?s=19 Ya bayyana cewa sun kagara su ga an kammala ginin titin jirgin kasar.   https://twitter.com/AnnahAbdullahy/status/1311063333462777859?s=19   Wata dai ta yi Addu'ar cewa Allah ka talauta duk wanda zai gujemi ya je auran 'yar Nijar.   https://twitter.com/Abkr_Maikudi/status/1311023746497548289?s=19   Ita kuwa wata cewa ta yi "mu kuma ku barmu da su wa?"   Saidai  ...
Mutane 158 Da Suka Makale A Kasar Nijar Sun Iso Gida Najeriya

Mutane 158 Da Suka Makale A Kasar Nijar Sun Iso Gida Najeriya

Siyasa
Wasu 'yan ciranin Najeriya' yan gudun hijirar an bar su a Jamhuriyar Nijar yayin sabon dawo da 'yan kasar Najeriya daga kasashen waje, a yayin da cutar corona ke ci gaba da yaduwa.   Akalla ‘yan Najeriya 158 suka makale a kasar Nijar sun iso gida, in ji Hukumar Kula da Jama’a (NIDCOM) a ranar Alhamis. An bar wasu 'yan Najeriya a baya bayan an tabbatar da suna dauke da cutar coronavirus. Dukkanin mutane 158 da ke cikin jirgin ana tsammanin za su kebence kansu daga isowa na tsawon kwanaki 14, daidai da ka'idojin kiwon lafiya da Ma'aikatar Lafiya ta umurce. Kungiyar Tarayyar Turai da kungiyar Hijira ta kasa da kasa tare da hadin gwiwar da tawagar Nijeriya a Nijar suka assasa kwaso mutanen. Hukumar ta kara da cewa dangi guda ba za su iya yin wannan balaguro ba ba...
Najeriya ta kulla yarjejeniyar sayo tataccen Man Fetur daga Nijar

Najeriya ta kulla yarjejeniyar sayo tataccen Man Fetur daga Nijar

Kasuwanci
A jamhuriyar Nijar yarjejeniyar kasuwanci ce aka kulla tsakanin kamfanin man fetur na Najeriya NNPC da kamfanin dillancin man fetur na Nijar SONIDEP, kan batun saida wa Najeriyar tataccen man da za ta yi amfani da shi cikin gida. Wannan dai ba ita ce yarjejeniyar farko ba da kasashen biyu suka kulla kan wannan batu ba, sai dai wannan karon za su dauki kwararan matakai don ganin yarjejeniyar ta mike.
Nijar ta dawo da ‘yan Najeriya 42 da suka shiga kasarta ba bisa ka’ida ba

Nijar ta dawo da ‘yan Najeriya 42 da suka shiga kasarta ba bisa ka’ida ba

Uncategorized
Kasar Nijar ta dawowa da Najeriya mutane 42 da suka shiga kasar tata ba tare da Izini ba, hakan ya farune tun daga 21 ga watan Maris 2020 yayin da Najeriya ta rufe iyakokinta saboda Annobar Coronavirus/COVID-19.   Hukumar kula da shigi da fici ta kasa reshen jihar Katsina dake Kongolam ce ta karbi wadannan 'yan Najeriya. Kwantirolan Jihar Katsina na hukumar, Abdullahi Abba Dalhatu ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace tuni har an gurfanar da 12 daga cikin mutanen a kotu bisa tuhumarsu da karya dokar shiga wata kasa daga Najeriya ba da izini ba.   Yace ana kan binciken sauran.
An sake bude makarantu a Nijar da Kamaru

An sake bude makarantu a Nijar da Kamaru

Siyasa
Kasashen Jamhuriyar Nijar da Kamaru sun sake bude makarantun boko ranar Litinin, bayan kwashe makonni da dama suna rufe. Hukumomi a kasashen biyu sun ce za a bar wani rukuni na dalibai su sake zuwa makarantu bayan sassauta dokar kulle. A Jamhuriyar Nijar, komawa makarantun za ta bai wa daliban damar daukar darusa tsawon kwana 45 kafin gudanar da jarrabawa. Ministan illimi mai zurfi na Nijar, Malam Yahouza Sadissou Madobi, ya shaida wa BBC cewa dole dalibai su rika sanya takunkumi da kuma daukar wasu matakan kare kansu kafin a bar su su shiga azuzuwa. A Jamhuriyar Kamaru, za a bar 'yan ajin karshe ne kawai su koma makarantun sakandare. BBChausa
Ranar Asabar ce Sallar Idi a Jamhuriyar Nijar

Ranar Asabar ce Sallar Idi a Jamhuriyar Nijar

Uncategorized
Majalisar Malaman addinin Musulunci da ke jamhuriyar Nijar ta ce ranar Asabar ne Sallah karama a jamhuriyar bayan ganin jaririn wata a garuruwa biyar a fadin kasar.   Wata sanarwa da Majlaisar ta fitar ta ce an ga jariirn watan na Shawwal a birnin Magaria da ke cikin jihar Damagaram wato Zinder da kuma a garuruwan Maine-Soroa da N'guiguimi da N'Gourti da ke cikin jihar Diffa mai iyaka da jihar Borno a Najeriya.   Haka ma jinjirin watan Shawwwal ya samu fita a garin Oungoudague da ke cikin yankin Tsibirin Gobir dake gundumar Gidan Rounji a jihar Maradin Katsina.     Majalisar ta ce ranar Asabar ne 1 ga watan Shawwal. Hakan na nufin al'ummar jamhuriyar Nijar sun yi azumi 29.     Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Saud...