fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: nishadi

Kana neman daukaka? : Karanta yanda zaka sameta kamar yanda Ummi Zeezee tayi bayani

Uncategorized
Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa Ummi Zeezee tayi bayani, kamar yanda tace, a addinance akan yanda mutum zai samu daukaka daga gurin Allah, ga jawabin nata kamar haka: "Salam, Ga kadan daga cikin "SIRRIN DAUKAKA " da Abubuwan da ke kawo daukaka a musulunce sune: 1.Riko da littafin Allah. 2.Bin Sunnar Manzon Allah SAW. 3. Nisanta da zunubai. 4.barin Zalunci. 5.takaituwa akan halal. 6. Yawan ambaton Allah. 7.kiyaye Farillai. 8.yawaita adduoi gun ambaton Allah. 9.gujewa haram. 10.yawan yin sallolin nafila musamman da tsakiyar dare. 11.yawan yin salati ga annabi Muhammad s.a.w. 12.bin iyaye. 13.yin hakuri ga abunda kake neman daukaka akai. 14.barin wulakanta mutane. 15.yawan godiya ga Allah a duk halin daka tsinci kanka aciki. Ammah mu sani Allah yana daukaka duk Wanda...

Rahama Sadau ta caccaki wani mutum da ya soki fim din hausa na farko da ta shirya(Rariya)

Uncategorized
Da alama fitacciyar korarriyar jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau bataji dadin sukar da wani bawan Allah ya yiwa fim din Hausa na farko data shirya da kantaba me suna Rariya, an ga wasu sakonnin mayar da martani da Rahamar ta wallafa a dandalinta na sada zumunta da muhawara na Twitter, inda take cewa "kana tunanin zan damu dan ka soki fim dina?, kai kadaine fa....a'a(bazan damuba). A cikin wani rubutun da tayi Rahamar tace "Idan beyi maka ba yayi ma wasu...kunyi rubutu nayi banza, amma dai dole akeso sai nayi magana shine aka kara yin wani". Bayan da aka koreta daga masana'antar fina-finan Hausane Rahamar ta koma gefe ta shirya fim din Rariya wanda ya samu wakar da ta sayar dashi tun kamin ya fito, wadda sanannen mawakin Hausar nan Nura M. Inuwa ya rera. Fim din Rarariya ...

Yadda ‘yar shekara 80 ta zagaye kasashen Afirka a mota

Uncategorized
A yayin da mutum ya kai shekara 80 a duniya, wani zai yi tunanin lokaci ya yi ya daina wasu abubuwa, sai dai batun ba haka yake ba ga wata dattijuwa Julia Albu 'yar kasar Afirka ta Kudu. Don kuwa a ranar da ta cika shekara 80 a duniya ne ta dauki 'yar tsohuwar motarta domin fara rangadi a nahiyar Afrika. Haka zalika ta dauki tanti da tukwane da kuma kayan sawa ne kafin ta dauki hanya a watan Yunin da ya gabata. Sai dai ta dawo Afirka ta Kudu inda take jiran bizarta ta zuwa Sudan kafin ta kara daukar hanya. Dattijuwar dai na rubuta bayanan abubuwan da ke faruwa a yayin wannan rangadi da suka hada da gudunmawar da ake bayarwa na wani shirin tallafi da take kira SHINE, wanda ake koyar da yara karatu. Wakilin BBC Mohammed Ali ya tambaye ta shin ko lokacin da za ta fara rangadin an ...

“Sai An Biya Ni Diyyar Naira Milyan Dari Kan Amfani Da Wakata Da Aka Yi Ba Da Izinina Ba”>>Inji Nazir M. Ahmad

Uncategorized
Shahararren mamawakin Hausan nan Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani Da Sarkin Waka ya nemi diyyar naira milyan dari daga wajen Ebonylife T.V.sakamakon yin amfani da wakar sa da suka yi a fim din su ba tare da izininsa ba. Ga cikkakiyar hirarsa da Usman Mu'azu kan lamarin. Da farko zamuso ka gabatar da sunanka?Sunana Naziru M. Ahmad (Sarkin Waka). Mun samu labari akwai wani gidan talabijin da yake amfani da wata waka taka ko za ka fada mana wace waka ce?Eh, sunan wakar bincike, muna ce mata bincike. Mun samu labarin suna amfani da wannan wakar bada izininka ba haka ne ko yaya abin yake?Hakane suna amfani da ita bada izinina ba kuma mun nemi su fada mana dalili sun yi shiru, shine muka ce za mu bi hanyar da ta dace domin karbar hakkinmu. Ta wace hanya kuka yi kokarin san...

Taron gidauniyar jaruman fina-finan Hausa

Uncategorized
Jaruman fina-finan Hausa na da dana yanzu kenan suka taru wajan wani taron gidauniyar Kannywood Celebrity, babu gamsasshen bayani dangane da makasudin taron amma anda jaruman sanye da kananan riguna da hula hana sallah sannan kuma suna rike da wasu kwalaye masu dauke da rubutun"yi aiki ka koya". Hadizan Saima ko bata lurabane ta rike nata kwalin sama a kasa? Sauran jaruman da suka halarci wannan guri sun hada da Saima Muhammad Ummi Nuhu, Maryam Jan kunne, Rukayya Dawayya da sauransu.