
Kimanin Yara miliyan 46 ‘yan Najeriya ba sa zuwa makaranta, – A cewar Hukumar NITDA
Hukumar bunkasa fasahar sadarwar ta zamani ta Najeriya (NITDA), ta bayyana adadin Yara Miliyan 46 ne basa zuwa Makaranta sakamakon barkewar cutar coronavirus a Najeriya.
Babban darektan hukumar NITDA, Kashifu Inuwa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya.
Haka zalika ya bayyana cewa A kalla a kwai Dalubai kimanin 24,372 da suka samu horo a karkashin Manhajar da hukumar ta samar dan tallafawa Dalubai a lokacin da suke zaman gida sakamakon cutar Covid-19.
Wadanda Suka halarci taron Sun hada Da Ministan Sadarwa Dakat Isa Ali Pantami tare da Sakataran hukumar hadi da Ministan Ilimi, tare da sauran mambobi dake Ma'aikatu biyun.