
Ba zamu Taba Lamunta ba: NLC ta gargaɗi gwamnatin Najeriya kan yunƙurin ƙarin kuɗin man fetur
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Ayuba Wabba, ya ce ƴan Najeriya ba za su iya jure sabon farashin ƙarin kuɗin man fetur ba.
Kalamansa na zuwa ne bayan shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, Mele Kyari ya shaida a jiya Alhamis cewa a kowanne wata gwamnati na biyan naira biliyan 100 zuwa 120 a matsayin tallafin mai, kuma hakan ba zai dore ba.
Don haka nan bada jimawa ba ƴan Najeriya za su koma sayen mai kan naira 235 maimakon 162 da ake saye a yanzu.
A wata tattaunawa da Jaridar Daily Trust ta Najeriya, Wabba ya ce ƴan Najeriya ba za su iya sayen fetur mai tsada ba saboda matsalolin rashin aikinyi da hauhawan firashi.
Ya kuma shaidawa jaridar cewa har yanzu ƴan ƙasar na farfadowa daga matsalolin tattalin arziki sakamakon annobar korona, don haka ƙarin kuɗin mai a wannan lokac...