fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Nnamdi Kanu

Dangote ne babbar matsalar Najeriya>>Nnamdi Kanu

Dangote ne babbar matsalar Najeriya>>Nnamdi Kanu

Tsaro
Shugaban haramtacciyar kungiyar dake son kafa kasar Biafra, IPOB, watau Nnamdi Kanu ya caccaki Attajirin Africa, Aliko Dangote kan sayarwa 'yan Najeriya Siminti da Tsada.   Ya bayyana cewa a kasashen Africa Dangote na sayar da Siminti a Farashi me Arha yayin da a Najeriya kuma ake sayar dashi a kusan ninkin farashin sauran kasashen.   A sakon da ya fitar ta shafinsa na Twitter, Kanu ya bayyana cewa a kasar Zambia, Dangote na sayar da Siminti akan Naira 1, 150 yayin da a Najeriya yake sayar dashi akan Naira 3000 zuwa 5000.   Ya kara da cewa, Dangote ne babbar Mataalar Najeriya.   The tweet reads: “In Zambia, Dangote sells cement for 55 Kwatcha (1150 Naira). But here in Nigeria, the same cement is going for 3,000 to 5,000 Naira.   “Dango...
Bidiyon yanda Inyamurai suka je ofishin jakadancin Kasar Ingila suna neman a kama Nnamdi Kanu

Bidiyon yanda Inyamurai suka je ofishin jakadancin Kasar Ingila suna neman a kama Nnamdi Kanu

Tsaro
Wata kungiyar inyamurai ta Je ofishin jakandancin kasar Ingila dake Najeriya inda suka nemia kamo shugaban kungiyar IPOB, dake son kafa kasar Biafra,  watau Nnamdi Kanu dan hukuntashi.   Kungiyar ta koka da cewa Kanu ya na zuga matasa suna kaiwa jami'an tsaro hari sannan kuma yana tunzurasu ana kashesu.   Yace abin takaici shine yana can kasar Ingila amma yana neman tadawa mutane hankali a Najeriya,  dan hakane suke kiran a hukuntashi.   https://www.youtube.com/watch?v=cfQ6Np5M9zU   A baya hutudole.com  Ya kawo muku Rahoton yanda sojoji suka kashe wasu tsagera 16 a Abia Wanda ake kyautata zaton 'yan IPOB ne    
Hotunan Tulin gawarwakin tsageran IPOB da sojojin Najeriya suka kashe

Hotunan Tulin gawarwakin tsageran IPOB da sojojin Najeriya suka kashe

Tsaro, Uncategorized
Gamayyar sojojin Najeriya da 'yansanda sun afkawa tsageran Kungiyar IPOB dake ikirarin son kafa kungiyar Biafra.   Jami'an tsaon sun kashe 16 daga cikin jami'an IPOB na kungiyar ESN a Abia.   Wata Majiyar tsaro ce ta bayyanawa Sahara Reporters haka a wata ganawa da suka yi inda tace an kai samamenne da daren ranar Talata.   Wannan kungiya ta ESN ana zargin itace ke da alhakin kaiwa jami'an tsaro a yankin hare-hare inda ta kashe akalla 'yansanda 20 da kona Ofisoshin su 3. Nigerian Army, Police Kill 16 IPOB's Eastern Security Network Operatives In Abia A joint operation of the Nigerian Army and police has led to the death of about 16 operatives of the Eastern Security Network (ESN), a military source told SaharaReporters on Wednesday. The source...
Ba yaki nake so ayi ba, Zaman Lafiya nake nema>>Nnamdi Kanu

Ba yaki nake so ayi ba, Zaman Lafiya nake nema>>Nnamdi Kanu

Uncategorized
Shugaban kungiyar IPOB sake son kafa kasar Biafra,  Nnamdi Kanu ya bayyana cewa ba yaki yake son a yi ba a kasarnan.   Yace abinda yake so shine ya kafa kasarsa ta Biafra cikin kwanciyar hankali. Kanu yace sai Asalin Mutane  Arewa suma sun farka akan Fulani sannan matsalar da ake ciki zata warware.   Kanu ya kuma bayana cewa, jami'an ESN da ya kafa dan su kare kansu ne ba dan tayar da hankali ba, yace amma fa ba wai tsoron yakin yake ba, ida ana so a yi a shirye suke. “Let these be clear: I come in peace, not war. #IPOB is committed to non-violence, but will never be cowardly. #ESN is about self-defense, not offense. My abiding mission is to restore #Biafra peacefully but if you want war, you will surely get it, sooner than later. THANK YOU.”   Kanu ...
Mun fi son Kasancewa tare a Najeriya fiye da Biafra da Nnamdi Kanu ke son samarwa>>Kungiyar Inyamurai

Mun fi son Kasancewa tare a Najeriya fiye da Biafra da Nnamdi Kanu ke son samarwa>>Kungiyar Inyamurai

Siyasa
Wata kungiyar Inyamurai dake zaune a Najeriya da kasashen waje, Coalition of South East Professionals Network in Nigeria and Diaspora ta bayyana cewa zaman su a Najeriya ya fi musu Alheri fiye da kasar Biafra da Nnamdi Kanu ke son samarwa.   Kungiyar ta zargi Nnamdi Kanu da canja mata Rijista wanda tace hakan ya tabbatar da zargin da take cewa yana amfanu da kungiyar ne kawai wajan Azurta Kansa.   Hakan na kunshene a cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Madumere Chika ya fitar a jiya, Asabar, Yace babu abinda ke tafiyar ta Kanu sai son kai. filed zero income in UK financial report”, ostensibly to pave the way for the personalisation of the group.   “How can Kanu change the registration status of IPOB to his personal business if he truly means well fo...
Idan muka kafa kasar Biafra zamu baiwa kasashen Togo, Benin, Ghana, Ivory coast da Gambia man fetur Kyauta>>Nnamdi Kanu

Idan muka kafa kasar Biafra zamu baiwa kasashen Togo, Benin, Ghana, Ivory coast da Gambia man fetur Kyauta>>Nnamdi Kanu

Siyasa
Shugaban 'yan Kungiyar IPOB dake neman kafa kasar Biafra,  Nnamdi Kanu ya bayyaba cewa idan suka kafa kasar tasu zasu rabawa kasashe Makwabta man Fetur kyauta.   Ya bayyana cewa zasu baiwa kasashen Ghana, Togo, Benin,  Ivory coast, da Gambia man fetur kyauta.   Yace zasu yi hakane dan nunawa Duniya cewa ba wai dan kudi ko kuma Man fetur suka kafa kasar ba, hakan ya fito ne daga bakin kakakin Kungiyar, Emma Powerful.   “Kanu equally promised to give free oil and gas to Ghana, Togo, Benin Republic, Ivory Coast, the Gambia and other countries in West Africa and Africa at large.   This is to prove to them that the agitation for Biafra autonomy is not driven by the quest to control oil money. Rather our struggle for self rule is borne out of our desir...
Ya kamata Gwamnati ta yafewa Nnamdi Kanu ya dawo Najeriya>>Kalu

Ya kamata Gwamnati ta yafewa Nnamdi Kanu ya dawo Najeriya>>Kalu

Tsaro, Uncategorized
Bulaliyar majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan Anambra, Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa, zai so gwamnatin tarayya ta yafewa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya dawo Najeriya.   Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai inda yace idan gwamnati ta bashi dama shi zai je har kasar Ingila ya tattauna da Kanu ya kuma sashi ya bar fafutukar kafa kasar Biafra. Yace Inyamurai basa son maganar kafa kasar Biafra Najeriya suke so wadda take dukulalliyar kasa da zata ci gaba.   Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kamfanin dillancin Labaran Najeriya, NAN.
Nnamdi Kanu ya fara gajiyane?: Ina ji kamar in bar fafutukar nan ta kafa kasar Biafra>>Injishi

Nnamdi Kanu ya fara gajiyane?: Ina ji kamar in bar fafutukar nan ta kafa kasar Biafra>>Injishi

Siyasa
Shugaban kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu ya bayyanawa magoya bayansa cewa shifa wani Lokacin ji yake kamar ya hakura da wannan fafutukar.   Ya bayyana hakane a wasikar da ya aikewa mabiyansa ta hannun me magana da yawunsa, Emma Powerful inda yace yana bin sahun annabi Isa(AS) ne. Hutudole ya ruwaito muku Kanu na martanine kan kisan 'yan kungiyar da DSS suka yi. Yace jinin wanda aka kashe bai zuba a banza ba dan ba zasu daina fafutuka ba har sai kasar Biafra ta kafu. Yace maimakon daina fafutukar zai ci gaba da yakar harin da jami'an tsaron Najeriya ke kaiwa kungiyar tasu.
Zamu kaddamar da ‘yan banga da zasu rika kare Inyamurai a Arewa>>Nnamdi Kanu

Zamu kaddamar da ‘yan banga da zasu rika kare Inyamurai a Arewa>>Nnamdi Kanu

Siyasa
Shugaban kungiyar dake fafutukar ganin ta kafa kasar Biafra,  IPOB, Nnamdi Kanu ya mayar da martani kan 'yan bangar da kungiyar fulani Makiyaya ta Miyetti Allah tace zata kafa a fadin kasarnan dan kare mutanen ta.   Kanu ta bakin me magana da yawunsa, Emma Powerful yace wannan abu ya zowa mutanen kudu da mamako amma su baizo musu da mamaki ba dan dama sun sha fada cewa tun a shekarar 2015 ne Fulani suka kaddamar da shirin mamaye Najeriya. Yace suna ta abinda suke so a Arewa shine suke so su kaddamar da irin wannan abu a kudu da sunan 'yan banga.   Yace to muddin 'yan Bangar na Miyetti Allah suka fara aiki to suma zasu kaddamar da Nasu 'yan bangar da zasu kare inyamurai a Arewa.   Kanu ya karyata cewa wai an kamashi.
Gwamnatin APC tana kokarin ganin Hausawa sun yi babakere a duk wani sha’anin kasarnan>>Nnamdi Kanu

Gwamnatin APC tana kokarin ganin Hausawa sun yi babakere a duk wani sha’anin kasarnan>>Nnamdi Kanu

Siyasa
Shugaban kungiyar masu fafutukar ganin sun kafa kasar Biafra(IPOB),  Mazi Nnamdi Kanu ya bayyana cewa gwamnatin APC kokarin da take kawai shine na ganin Hausawane a saman duk wata harkar kasarnan.   A sanarwar da kungiyar ta fitar ta bakin me maganada da yawunta, Emma Powerful yace shugaban kungiyar na ganin APC na cire duk wasu kwararrun da suka iya aiki tana dora Hausawa. Yace koda a baya ya gayawa mutanensa cewa Za'a baiwa Fulani makiyaya makamai inda zasu rika mamayar kasashen kudu da sunan kiwo wanda yace a karshe manufar hakan shine musuluntar da Najeriya.   Yace gashi kuma hakan ta faru, yace abinda ya rage kawai shine a hukumance a fito a bayyana cewa kasar Najeriya ta zama ta musulmai.   Kanu yace amma fa ba zai hakura ba sai ya tabbatar da ...