fbpx
Tuesday, December 1
Shadow

Tag: NNPC

Da Gangan Muka Kulle matatun man Najeriya>>Shugaba NNPC

Da Gangan Muka Kulle matatun man Najeriya>>Shugaba NNPC

Uncategorized
Shugaban kamfanin mai na kasa, NNPC, GMD Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa suna sane suka kulle Matatun man Najeriya.   Yace dalili kuwa shine ba zasu iya ci gaba da gudanar dasu ba. Yace da farko akai matasalar rashin aiki da matatun man suke yanda ya kamata.   Yace domin matatun su fara aiki yanda ya kamata a kaso 70 cikin 100 sai an rika kai musu ganga 170,000 ta danyen mai kullun. Yace amma ayyukan masu fasa bututun mai ba zai bari ba. Yace cikin wata 1 kawai saida suka gyara ayyukan barnar masu fasa bubutun mai da ya kai 80. Yace kuma daga watan Janairu zuwa June sun tafka Asarar mai ta Biliyan 43 wadda masu fasa bututun suka jawo.   Ya bayyana hakane a gaban kwamitin majalisar tarayya dake kula da harkar mai inda yace majalisar ta yi kokarin amincewa da...
Shugaba Buhari baya tsoma baki a ayyukan NNPC – Mele Kyari

Shugaba Buhari baya tsoma baki a ayyukan NNPC – Mele Kyari

Siyasa
Babban Manajan Daraktan Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Malam Mele Kyari, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai taba tsoma baki a cikin ayyukan Kamfanin ba. Haka zalika ya bayyana cewa, kamfanin  na da cikakken goyon baya daga shugaban kasa wajan gudanar da ayyukan kamfanin yadda ya kamata. Kyari ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Juma'a a Abuja. Kamar yadda ya bayyana da cewa, "Ya shafe tsawan shekaru 26 a ma'aikatar, inda yayi  aiki da manayan shugabanin Ma'aikatar tsawan shekaru 15, amma a cewar sa bai  taba ganin shugaban da baya ka tsalanadan  a al'amuran Ma'aikatar ba kamar shugaba Buhari. Inji shi. Shugaban ma'aikatar man na kasa yace, kamfanin ya mayar da hankali ne kan bunkasa iskar gas a matsayin wata babbar hanyar samar da makamashi do
Kwamitin majalisan wakilai ta gayyaci NNPC da CBN kan zargin bacewar tiriliyan N3.2 na kudin mai

Kwamitin majalisan wakilai ta gayyaci NNPC da CBN kan zargin bacewar tiriliyan N3.2 na kudin mai

Siyasa
Majalisar wakilai ta gayyaci Babban Manajan Darakta na Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mista Mele Kyari, da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele kan zargin rashin shigar da kudaden shiga na Naira tiriliyan 3 da biliyan 235 (dala biliyan 19.253) da aka samu daga sayar da danyen mai na cikin gida a shekarar 2014. Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin asusun, Mista Wole Oke, ya bayar da wannan umarnin a yayin sauraren binciken binciken da aka yi game da tambayoyin binciken da ofishin Odita Janar na Tarayya (AuGF) ya bayar na lokacin da ake dubawa. Sammacin ya zo ne kwanaki 10 kacal bayan da shugaban kamfanin na NNPC ya ki mutunta goron gayyatar da aka aike masa a makon da ya gabata, kan zargin cire dala biliyan 20.301 ba bisa ka’ida ba daga asusun rarar man fetu
Majalisa ta nuna bacin ranta kan kin gurfana a gabanta da shugaban NNPC yayi dan yin bayanin karkatar da Biliyan 21.686 na NLNG

Majalisa ta nuna bacin ranta kan kin gurfana a gabanta da shugaban NNPC yayi dan yin bayanin karkatar da Biliyan 21.686 na NLNG

Siyasa
Majalisar wakilai a karkashin kwamitin dake kula da kudaden al'umma ta bayyana bacin ranta kan kin bayyana a gabanta da shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari yayi dan bayanin karkatar da wasu kudi.   Ana zargin an karkatar da kudin ribar kamfanin NLNG Dala Biliyan 21.686 kamar yanda babban Odita janar na kasa ya mikawa majalisar Korafi wanda kuma kamfanin NNPC dinne ake zargi.   Shugaban kwamitin, Wole Oke ya bayyana cewa shi da sauran abokan aikinsa basu ji dadin kin bayyanar Mele Kolo kyari ba dan ya musu bayanin yanda aka kashe kudin.   Yace babu wanda ke da ikon taba kudij ribar da aka samu na kamfanin NLNG da ya kamata a sakasu Asusun gwamnati. Ana zargin an karkatar da kudinne aka yi wani aiki na daban dasu. “I, and members of the Committee, are not h
Kamfanin man fetur na Kasa NNPC ya karya ta Labarin da A ke yadawa kan yi wa shafin kutse

Kamfanin man fetur na Kasa NNPC ya karya ta Labarin da A ke yadawa kan yi wa shafin kutse

Tsaro
A wani sako da Kamfanin Man fetur na kasa wato NNPC ya fitar a ranar litinin, ya bayyana cewa har yanzu shafin Ma'aikatar na nan daram babu wani barazanar tsaro ga shafin. Martanin ya biyo bayan sakamakon labaran da a ka yada game da yiwa shafin kamfanin kutse. Sai dai Kamfanin ya tabbatar da cewa shafin yana cikin tsaro hasalima shafin ba za'a iya yi masa kutse ba, sakamakon na cikin tsaro.  
Ba kulle kamfanin mai na kasa, NNPC zamu yi ba, sayar dashi zamu yi>>Gwamnati ta yi karin haske

Ba kulle kamfanin mai na kasa, NNPC zamu yi ba, sayar dashi zamu yi>>Gwamnati ta yi karin haske

Siyasa
Karamin Ministan man Fetur, Timipre Sylva ya bayyana cewa ba kulle kamfanin mai na kasa za'a yi ba kamar yanda ake yayatawa.   Yace kudirin dokar gyaran bangaren Man Fetur da aka mikawa majalisa zai bada damar sayar da kamfanin na NNPC ne ba kulleshi ba, yace wannan na daya cikin shirin da gwamnati take na zare hannunta daga harkar man fetur din. Ya bayyana hakane bayan ganawa da shuwagabannin majalisar. Yace sayar da kamfanin man Fetur din zai bayar da damar yin gasa tsakanin kamfanonin man wanda kuma abi  alheri ne ga Najeriya.   Yace hakanan garuruwan da kamfanonin suke zasu amfana da wannan sayarwa sannan kuma za'a hade wasu ma'aikatun gwamnatin tarayya waje guda.
Kwanannan zamu bude wajan sayar da Gas na musamman dan saukakawa ‘yan Najeriya tsadar Man fetur>>NNPC

Kwanannan zamu bude wajan sayar da Gas na musamman dan saukakawa ‘yan Najeriya tsadar Man fetur>>NNPC

Siyasa, Uncategorized
Kamfanin Mai na kasa, NNPC ya bayyana cewa kwanannan zasu kaddamar da gidajen sayar da Gas.   Hakan ya fitone daga bakin daya daga cikin Daraktocin kamfanin Man na kasa, Dr. Kennie Obature inda yace gas din zai zama kamar Man fetur ne da ake sakawa a Motoci. Kamfanin NNPC ya bayyana saboda zare hannun gwamnati daga harkar mai ta kasa ne yasa zata yi haka dan saukakawa 'yan Najeriya wahalar tsadar Man fetur.
Najeriya ta samu rarar dala Miliyan 400 daga cire tallafin man fetur>>Kyari

Najeriya ta samu rarar dala Miliyan 400 daga cire tallafin man fetur>>Kyari

Kiwon Lafiya
Shugaban kamfanin mai na kasa, NNPC, Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa Najeriya ta yi nasarar samun kudu har dala miliyan 400 daga cire tallafin man fetur daga kasafin kudin 2020.   A watan Maris na wannan shekarar ne aka cire tallafin man. Kyari yace koda farashin mai ya tashi a kasuwannin Duniya da wuya a sake dawo da tallafin man. Yace a baya mutane da dama sun ta kira da a cire tallfin man saboda mutane da ake sakawa saboda su baya kaiwa garesu, wasu kalilan masu kudi ne ke amfana da lamarin.   Yace yanzu za'a yi amfani da kudin wajan inganta ilimi ko gina ababen ci gaban al'umma kamar titi.   Yace NNPC na kokarin ganin matatun manta sun dawo aiki inda yace suna tunanin baiwa 'yan kasuwa ita ko kuma hada hannu su yi aiki tare kamar yanda akawa LNG....
Kamfanin mai na kasa,NNPC ya sallami ma’aikata 850>>Kungiyoyin Kwadago

Kamfanin mai na kasa,NNPC ya sallami ma’aikata 850>>Kungiyoyin Kwadago

Uncategorized
Kungiyoyin kwadago na kamfanin mai na kasa, PENGASSAN da NUPENG sun koka kan korar ma'aikata 850 da suke taimaka musu wajan aiki.   A sanarwar da suka fitar tare, kungiyoyin sun ce ana tsaka da Coronavirus/COVID-19 aka sallami ma'aikatan ba tare da wani tanadi na basu kudin sallama ba. Sunce yawancin wadannan ma'aikata sun yi aiki na tsawon shekaru 10 zuwa 15 da Kamfanin mai na kasa dan haka ya kamata a biyasu kudin sallama.   Kungiyar tace barazanar sallamar aiki da shugaban kamfanin ke yi ba wai wani Sabon abu bane dan sun ganshi ma ya fara faruwa amma abinda suke so shine a biya mutane kudin hakkinsu na sallama.
Majalisar Wakilai ta gayyaci kamfanonin NNPC da NLNG bisa zargin cire Dala Biliyan 1.05 ba bisa ka’ida ba

Majalisar Wakilai ta gayyaci kamfanonin NNPC da NLNG bisa zargin cire Dala Biliyan 1.05 ba bisa ka’ida ba

Siyasa
Majalisar Wakilai na bincikar kamfanin mai na NNPC a kan zargin cirar Dala biliyan 1.05 daga ribar iskar gasa ba bisa ka’ida ba.   Majalisar ta bukaci shugabannin kamfanin NNPC da kuma kamfanin iskar gas na kasa (NLNG) su bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan kudaden. Maganar ta taso ne sakamakon kudurin da Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu (PDP, Delta), ya gabatar. Elumelu ya zargi NNPC da yin gaban kansa ba tare da tuntubar majalisa ba wajen cirar Dala biliyan 1.05 daga asusun ribar NLNG, sabanin abin da doka ta tanada. Dokar ta yi tanadi cewa NNPC, wanda ke wakiltar Gwamantin Tarayya a Kwamitin Amintattu na NLNG ba zai ciri kudi daga asusun ba sai da amincewar majalisa. Zauren majalisar ya umarci kwamitinsa na asusun gwamnati ya gayyanci NNPC da