fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: NSIP

NSIP sun yi kira ga shugaba Buhari ya kori Sadiya Umar Farouk daga aiki saboda rashin biyansu alwus dinsu

NSIP sun yi kira ga shugaba Buhari ya kori Sadiya Umar Farouk daga aiki saboda rashin biyansu alwus dinsu

Siyasa
Ma'aikatan NSIP dake kula da ayyukan tallafawa gwamnatin tarayya da suka hada da N-Power, da ciyar da dalibai abincin makaranta dadai sauransu sun koka kan yanda har yanzu ba'a biyasu alawus din da suke bi na watannin Maris da Afrilu ba.   Sun bayyana rashin jin dadinsu inda sukace har na watan Mayu ba ba'a biyasu ba. Wasu da suka yi magana da Sahara Reporters kamar yanda Hutudole ya samo sun bayyana cewa aikinsu kenan tun da suka gama makaranta amma rashin biyansu albashin yasa basa iya ci gaba da dawainiyar rayuwarsu yanda ya kamata.   Saidai wata Majiya daga ma'aikatar jinkai da kula da Ibtila'i ta bayyana cewa ana aiki kan biyan ma'aikatan na NSIP.