
Gaskiya ba’a min Adalci ba, a dawo min da Laila kawai>>Mahmood na shirin Labarina
Tauraron fina-finan Hausa, Nuhu Abdullahi wanda ya fito a matsayin Mahmood a cikin shirin Labrina da ake nunawa a tashar Arewa24 ya bayyana cewa gaskiya ba'a masa Adalci ba.
Ya bayyana hakane ta shafinsa na Instagram, abokin aikinsa, Ali Nuhu ya tambayeshi, kai kawa Sumayya Adalci?
Ya bashi Amsar cewa, Yallabai Yanayi ne ya zo da haka amma dai yanzu a dawo min da Laila.
Shima dai me bada Umarnin shirin, Malam Aminu Saira ya bayyana cewa, Allah ya kiyaye gaba ya sa Kaffara ya sa ya zama Darasi ga wasu.
https://www.instagram.com/p/CJW5jVCJQA4/?igshid=x9vepsod9ts