fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Nuhu Bamalli Polytechnic

Yan Bindiga Sun Sace Wasu Ma’aikatan Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Na Nuhu Bamali Dake Jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Sace Wasu Ma’aikatan Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Na Nuhu Bamali Dake Jihar Kaduna

Tsaro
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu ma’aikatan kwalejin fasaha ta Nuhu Bamali da ke Zariya a jihar Kaduna. Wadanda aka sace din, wani malami, da kuma wani ma'aikacin da ba na ilimi ba an sace su ne a ranar Asabar daga rukunin gidajen ma'aikatansu da ke cikin makarantar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce‘ yan bindigar da yawansu sun mamaye gidajen ma’aikatan kwalejin fasaha ta Nuhu Bamali da misalin karfe 10:00 na dare. a ranar Asabar. Ya ce ‘yan bindigar sun tafi da ma’aikata biyu zuwa wani wurin da ba a sani ba. Yan bindigar sun raunata wasu mutane biyu kuma tuni aka garzaya da su zuwa asibiti don yi musu magani. Jalige ya ce ja...