fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Tag: Nuhu Ribadu

Shugaba Buhari ya taya tsohon shugaban hukumar EFCC  Nuhu Ribadu murnar cika shekara 60

Shugaba Buhari ya taya tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu murnar cika shekara 60

Uncategorized
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Nuhu Ribadu murnar cika shekaru 60 a duniya. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Ribadu ya cika shekara 60 a Duniya a yau Asabar. Shugaba Buhari  ya bayyana haka ne, a  cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina , ya fitar a Abuja ranar Juma'a. Hakanan shugaba Buhari ya, yabawa tsohon shugaban hukumar a matsayin jajirtacce wanda ya sadaukar da kansa domin hidim tawa kasa. A karshe yayi fatan Allah ya karu yawan shekaru masu amfani.
Allah Sarki:Diyar Nuhu Ribadu ta bada Hakuri kan shigar da ta yi a Bikinta

Allah Sarki:Diyar Nuhu Ribadu ta bada Hakuri kan shigar da ta yi a Bikinta

Siyasa
Fatima Nuhu Ribadu ta nemi afuwa kan tufafin da ta sa a ranar ɗaurin aurenta da suka janyo cece-kuce musamman a shafukan sada zumunta na intanet.   A ranar Asabar ne aka ɗaura wa Fatima Ribadu, ƴar Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC aure da Aliyu Atiku Abubakar ɗan tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar. Hotunan auren sun ta yawo a shafunan intanet na sadarwa, saboda ƴaƴan manyan ƴan siyasa ne a Najeriya.   Sai dai kwalliyar da ƴar gidan Ribadu ta yi a ranar ɗaurin auren ce ta janyo ce-ce-ku-ce musamman farin tufafin da ta sa da wasu ke ganin sun nuna tsaraicinta.   A cikin saƙon da ta wallafa a Instagram, Fatima Ribadu ta ce ta yi nadama kan yadda hotunan suka fita shafukan sada zumunta ba da son ranta ba.  ...
Hotuna: Auren ‘yar Gidan Nuhu Ribadu da dan Atiku Abubakar ya tara ‘yan PDP da APC a waje daya

Hotuna: Auren ‘yar Gidan Nuhu Ribadu da dan Atiku Abubakar ya tara ‘yan PDP da APC a waje daya

Siyasa
SIYASA BA GABA BA: Yadda Jiga-jigan Jam'iyyun APC Da PDP Suka Hadu A Wurin Daurin Auren Dan Atiku Abubakar Da 'Yar Nuhu Ribadu   An daura auren Aliyu Atiku Abubakar ne da Fatima Nuhu Ribadu a yau Asabar a Aso Drive dake Abuja.   A hotunan za'a iya ganin Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso,  Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai,  Tsoho  Mataimakin shugaban kasa,  Alhaji Atiku Abubakar,  Tsohon gwamnan jihar Naija, Babangida Aliyu, dan takarar gwamnan Kano a zaben 2019, Abba K. Yusuf, wands aka fi sani da Abba Gida-Gida, dadai sauransu. Daga Aliyu Ahmad