fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: NUJ

Kungiyar ‘yan jaridu NUJ Ta bukaci Rundunar ‘Yan Sanda ta kamo Wadanda Suka Harbi Dan Jarida A Jihar Kogi

Kungiyar ‘yan jaridu NUJ Ta bukaci Rundunar ‘Yan Sanda ta kamo Wadanda Suka Harbi Dan Jarida A Jihar Kogi

Crime
Shugaban kungiyar ‘yan Jaridu na kasa (NUJ), Mista Chris Iziguzo, ya roki rundunar‘ yan sanda ta jihar Kogi da ta tona asirin wasu bata gari, wadanda suka harbi Wakilin Jaridar Sun na jihar, Mista Emmanuel Adeyemi, a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba , 2020 a Lokoja. Ya bukaci 'yan sanda da su sauke nauyin da ya rataya a wuyan su, tare da kawo karshan halin da a ke ciki na rashin tsaro. Shugaban NUJ ya kuma yi tir da harin da a ke kaiwa ga wasu kafafen labaru, inda ya kira da cewa hakan abun ta kaici ne kasancewar yanzu lokaci ne na Dumukuradiya.