fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Nura M. Inuwa

Waƙata ta taɓa mayar da aure da ceton rai>>Nura M Inuwa

Waƙata ta taɓa mayar da aure da ceton rai>>Nura M Inuwa

Nishaɗi
Nura M Inuwa, na ɗaya daga cikin mawaƙan zamani wanda za a iya cewa ya shahara a ƙasar Hausa, kuma ya yi wakoƙi musamman na soyayya da dama.   A wata tattaunawa da BBC ta yi da mawaƙin a Shafin Instagram da Facebook, mawaƙin ya bayyana cewa ya fara waƙa ne tun a 2007, kuma ya fara ne da waƙar siyasa. A cewarsa, a halin yanzu waka ta zama sana'a, kuma hanya ce da zai iya isar wa mutane sako musamman idan ya ga ɓarna sai ya gyara.   Ya ce wakokinsa da dama sun kawo sauyi, domin akwai wata waƙarsa mai suna 'Ga Wuri Ga Waina' wadda a ciki ne ya yi magana kan makomar wanda ya kashe kansa.   Ya ce a sakamakon haka "akwai waɗanda suka kira ni suka ce na yi ceto, ma'ana na ƙwaci wata yarinya daga halaka, tana ƙoƙarin halaka kanta ta ji waƙar 'Ga Wuri Ga Waina'...