
Yan Bautar Kasa 11 Sun Kamu da Cutar COVID-19 a Sansanin Yan Bautar Kasa na Jihar Taraba
Akalla mambobi masu bautar kasa (NYSC) goma sha daya ne suka kamu da cutar Coronavirus a sansanin yan bautar kasa na Jihar Taraba.
Kwamishinan lafiya na jihar Taraba, Innocent Vakkai ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar.
Vakkai ya ce, 'yan yi wa kasa hidiman da suka kamu an tabbatar da cewa ba su nuna wata alama kuma suna amsar magani a wani kebabben wuri a jihar.
Kwamishinan ya yi bayanin cewa an yi wa membobin bautar kasar gwajin ne bisa umarnin da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayar cewa duk mambobin shirin za a gwada su a lokacin da suka iso sansanonin daban-daban.
An gano yan bautar kasa 11 tare da cutar a jihar Taraba lokacin da suka isa sansanin.
”Don haka a matsayin wani bangare na jagororin kwami...