fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Obadia Mailafiya

Bafa zan canja abinda na fada ba cewa wani gwamnane kwamandan Boko Haram>>Obadiah

Bafa zan canja abinda na fada ba cewa wani gwamnane kwamandan Boko Haram>>Obadiah

Tsaro
Bayan kwashe awanni 6 yana tsare a komar 'yansansan farin kaya, DSS tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, CBN,  Obadiah Mailafiya ya nace akan cewa ba zai canja ikirarinsa ba.   Bayan sakinshi ya gana da manema labarai inda yace koda zai mutu ba zai daina magana akan matsalar taaron Najeriya ba da kare muradun marasa karfi. Hutudole ya fahimta a rahoton da punch ta samar cewa wani babban limamin Kiristoci ne ya tsayawa Obadiah  DSS suka sakeshi. Saidai kungiyar gwamnonin Arewa ta bukaci da cewa wannan zargine da bai kamata a barshi hakanan ba, ya kamata a Bincikeshi. Hutudole ya ruwaito muku cewa, shugaban kungiyar gwamnonin, Kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong yace ba zasu bari wanan zargi ya wuce ba haka kawai.   Yace kullun suna taro dan gan...
A karshe dai DSS ta saki Obadia Mailafiya

A karshe dai DSS ta saki Obadia Mailafiya

Tsaro
Bayan awanni 6 yana a cikin Ofishin Hukumar 'yansandan farin kaya inda suke tuhumarsa akan kalaman cewa akwai gwamnan Arewa a Boko Haram,  tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, CBN,  Obadia Mailafiya ya shaki Iskar 'yanci.   Da musalin wajan karfe 12 na ranane ya je ofishin DSS dake garin Jos inda shi kadai da lauyansa, Pius Akumo SAN suka samu shiga ofishin DSS din. Hutudole ya fahimci cewa, daga baya magoya bayansa sun fara zanga-zangar a sakeshi. Da misalin karfe 6 na yammane aka saki Mailafiya daga Ofishin DSS din. Ya bayyanawa Manema labarai cewa zai ci gaba da tsayawa wanda basu da gata wajan karesu.   Ya bayyana cewa duk wani matashi daga duk inda ya fito nasa ne sannan kuma ya nemi masoyansa da kada su yi kasa a gwiwa wajan fafutuka.