fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Obadiah Mailafiya

Wasu manyan kasashen Duniya na son wargaza Najeriya>>Obadiah Mailafiya

Wasu manyan kasashen Duniya na son wargaza Najeriya>>Obadiah Mailafiya

Uncategorized
Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya,  CBN, Obadiah Mailafiya ya  bayyana cewa wasu manyan kasashen Duniya na son wargaza Najeriya.   Ya bayyana hakane yayin da yake magana akan matsalar tsaro a mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda yace Ko kusa ba za'a hada zamanin Abacha da na Buhari ba, idan da Abacha ne da ba zai amince da wannan abinda ke faruwa ba.   Yace Turawan yamma sun hurewa wasu mutane kunne inda suka gaya musu cewa dole sune zasu mulki kasarnan, kuma suka basu makamai.  Yace sun shiga daji sunawa mutane kisan kare dangi. A former Deputy Governor of the Central Bank of Nigeria, Dr. Obadiah Mailafia, Wednesday accused world powers of trying to destroy the country. In today’s international system, the four great powers according t...
Kotu tayi watsi da bukatar Mailafia na hana ‘Yan Sanda binciken sa

Kotu tayi watsi da bukatar Mailafia na hana ‘Yan Sanda binciken sa

Siyasa
Wata babbar kotun jihar Filato ta yi watsi da bukatar Dr. Obadiah Mailafia wanda ya nemi hana rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta hanyar sashin binciken manyan laifuka daga binciken shi a wani lamari wanda  ma’aikatar tsaro ta DSS ke bincika. Da yake yanke hukunci a kan karar a ranar Talata, Mai Shari’a, Arum Ashom na Babbar Kotun 5, Jos ya yi watsi da karar saboda rashin cancanta. ‘Yan sanda sun ce suna“ bincike kan karar da sunanka ya fito fili, ”amma da suka samu wasikar gayyata, sai tawagar lauyoyin Mailafia karkashin jagorancin Pius Akubo SAN suka garzaya kotu suna neman a yanke hukunci a kan wasikar kamar yadda suka bayyana gayyatar a matsayin tsoratarwa, cinmutunci, tsanantawa da bita da kulli. Idan za a tuna cewa Dr. Mailafia a wata hira da aka yi da shi a red...
Allah yasa wannan gayyatar itace ta karshe da DSS zasu min>>Obadiah Mailafiya

Allah yasa wannan gayyatar itace ta karshe da DSS zasu min>>Obadiah Mailafiya

Uncategorized
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma tsohon Mataimakin Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya ya bayyana cewa yana fatan Allah yasa wannan ce gayyatar karshe da DSS zasu masa.   Mailafiya ya bayyana a karo na 3 a ofishin DSS dake Jos kan kalaman da yayi yayin hira da wata gidan Rediyo cewa wani Gwamnan Arewa, da bai bayyana sunansa ba, shine Kwamandan Boko Haram. A jiyan, Masoyansa da dama ne suka je Ofishin DSS din dan nuna soyayya a gareshi. Bayan ganawa da DSS, Obadiah Mailafiya ya koka da cewa mutane da dama sun fadi abinda ya fi nashi Muni amma sai shine aka gayyata.   Yace yana fatan wannan gayyatar ta zama ta karashe da za'a masa abinda yake kira akai shine kawai a daina kashe-kashen da ake.
Bani da shaida kan ikirarin da na yi>>Obadiah Mailafiya

Bani da shaida kan ikirarin da na yi>>Obadiah Mailafiya

Uncategorized
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya ya bayyana cewa bashi da Hujjar da zai iya bayarwa kannikirarin da yayi.   Ya bayyana hakane a ranar Litinin biyo bayan gayyatar da DSS suka masa zuwa Ofishinsu. Yace baida hujjar da zai iya bayarwa kan zargin da yayi cewa akwai hannun gwamnati a kashe-kashen da ake yi a Najeriya. Ya dai yi zargin cewa akwai kwamandan Boko Haram da Gwamnan Arewa ne, wanda hakane tasa DSS din suka gayyaceshi har sau 3.   Bayan ganawa da DSS din da yayi a yau yace an karramashi lokacin ganawar kuma babu wani cin zarafi da aka masa, yace amma da zai samu dama da ya gyara wancan kalami nashi da yayi a baya.   Ya kuma bayyana cewa akwai sanda yaga wasu suka shawa...
Boko Haram: A karo na 3 DSS Sun sake gayyatar Obadiah Mailafiya

Boko Haram: A karo na 3 DSS Sun sake gayyatar Obadiah Mailafiya

Siyasa, Tsaro
Hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS a karo na 3 ta sake gayyatar tsohin mataimakin Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya.   DSS ta gayyaci Mailafiya zuwa ofishinta dake Jos. Lauyansa, Yakubu Bawa ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau, Juma'a. Tun farko dai DSS ta gayyaci Mailafiya ne saboda kalaman da yayi cewa akwai gwamnan Arewa kwamandan Boko Haram,  saidai bai fadi suna ba.   Lauyansa yace abinda ake wa Mailafiya bai kamata ba saboda yayi aikin banki da koyarwa a kasashen waje amma ba'a gaba samunsa da wani laifi ba amma gashi ana ta masa bita da kulli akan wannan lamari.
Yanzu-Yanzu: Obadiah Mailafiya yayi Murabus daga Mukaminsa sannan ba zai amsa gayyatar ‘yansanda ba

Yanzu-Yanzu: Obadiah Mailafiya yayi Murabus daga Mukaminsa sannan ba zai amsa gayyatar ‘yansanda ba

Tsaro
Tsohon mataimakin Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya ya bayyana cewa ya ajiye mukaminsa a matsayin shugaban hukumar kula da tsare-tsare ta kasa, NIPSS.   Ya bayyana hakane a wata hira da yayi ta waya da Daily Trust inda ya bada dalilin cewa ba zai iya ci gana da rike wani mukami ba yayin da ake wa kabilarsa kisan kare dangi. Yace ya gabatarwa da hukumar takardar ajiye aikinsa sannan kuma sun amince. Hakanan Mailafiya ta bakin lauyansa, Yakubu Bawa ya kalubalanci gayyatar da 'yansanda suka masa inda yace an take hakkinsa.   Dan hakane yace zai kai kara kotu dan kotun ta dakatar da wannan gayyara. Hutudole ya kawo muku cewa Obadiah Mailafiya ya fara shiga matsala ne tun bayan da yayi ikirarin cewa akwai gwamnan Arewa da shine Kwamandan Boko Ha...
Kuma Dai: Yan Sanda Sun Gayyaci Mailafia Game Da Magana Kan Boko Haram

Kuma Dai: Yan Sanda Sun Gayyaci Mailafia Game Da Magana Kan Boko Haram

Tsaro
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gayyaci tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Dakta Obadiah Mailafia, domin amsa tambayoyi. A cewar wata wasika mai dauke da ranar 20 ga Agusta, 2020 wacce Umar Mamman Sanda, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda ya sanya wa hannu, a madadin Mataimakin Sufeto-Janar na' yan sanda (Sashen Binciken Laifuka), ana sa ran Mailafiya zai kasance a Rundunar. Babban hedikwata a Abuja da karfe 11 na safiyar Litinin 24 ga Agusta, 2020. Hukumar DSS ta taba gayyatar Mailafia har sau biyu a kan ikirarin da yayi cewa wani gwamna daga Arewa ne kwamandan kungiyar Boko Haram. Ya yi wannan ikirarin ne yayin da ake hira da shi a wani gidan rediyo da ke Abuja.
DSS ta saki Mailafiya bayan kwashe mintima 40 ana tuhumarsa

DSS ta saki Mailafiya bayan kwashe mintima 40 ana tuhumarsa

Siyasa
Rahotanni dsga jihar Filato sun bayyana cewa ta saki Obadiah Mailafiya data gayyata yau a karo na 2 baya shafe mintuna 40 ana tuhumarsa.   Saidai bayan fitowarsa daga ofishin DSS din, Mailafiya ya bayyana ta bakin lauyansa cewa an bashi kulawar data kamata babu wani alamar cin zarafi. Lauyan nasa, Yakubu Bawa ya bayyana cewa an ci gaba da maganane akan lamarin da yasa aka gayyaci mailafiya tun farko.
Yanzu haka Obadia ya sake kai kansa Ofishin DSS

Yanzu haka Obadia ya sake kai kansa Ofishin DSS

Siyasa
Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, CBN,  Obadiah Mailafiya ya kai kansa ofishin DSS da misalin karfe 12:10 na yammacin yau.   A makon da ya gabata, Mailafiya da ya je ofishin DSS sai da ya kwashe awanni 6 ana tsare dashi ana masa tambayoyi kamin a sakeshi ba tare da sharadi ba. Hutudole ya samo muku daga TheNation cewa, a yau Mailafiya yaje ofishin DSS tare da matarsa, Margaret Vou da kuma lauyansa, Yakubu Bawa. Da yake magana da manema labarai kamin shiga Ofishin DSS din, Mailafiya ya bayyana cewa bai san dalikin kara gayyatarsa ba amma a matsayinshi na dan kishin kasa shine ya ga dacewar ya amsa wannan gayyata.
DSS ta sake gayyatar Obadiah Mailafiya

DSS ta sake gayyatar Obadiah Mailafiya

Tsaro
A karo na 2, hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS ta sake gayyatar tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya.   A baya dai DSS ta gayyaci Mailafiya saboda ikirarin da yayi a wani gidan rediyo cewa akwai gwamnan Arewa kwamandan Boko Haram. Hutudole ya ruwaito lauyan Mailafiya,  Yakubu Bawa yana tabbatar da sabuwar gayyatar da DSS sukawa Mailafiya. Yace da misalin karfe 12 na ranane suka bukaci Mailafiya ya sake zuwa ofishin nasu dake Jos a ranar Litinin.  Yayi fatan cewa maganar da zasu yi ba zata wuce wadda aka yi a baya ba, kamar yanda NAN ta ruwaito.